Babaji

5687 Posts

Kano: ‘Yan daba sun raunata mutane da sace kayayyaki a kasuwar Farm Centre

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Al'umma sun shuga firgici a cikin garin Kano a yau Litinin, yayin da wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun kai hari a shahararriyar kasuwar sayar da wayoyin hannu ta Farm Centre da tsakar rana, lamarin da ya yi sanadin raunata mutane da dama da sace kayayyaki masu daraja. Rahotanni sun ce maharan sun afka wa kasuwar ne, wadda jama'a da dama ke hada-hada, inda suak firgita 'yan kasuwar da kwastomomi da makamai masu kaifi tare da karɓe iko da wani sashen yankin. A ruwaito cewa, a sashen Yoyo Plaza, sun riƙa dukan…
Read More

Tijjaniyya ta ƙalubalanci ci gaba da tsare Sheikh Sani Zariya duk da umarnin kotu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗariƙar Tijjaniya a Nijeriya, ta koka game da cigaba da tsarewa da gurfanar da ɗaya daga cikin jagororinta, Sheikh Abdulƙadir Sani Khalifa Zariya, inda ta bayyana hakan a matsayin takura da kira da a bi umarnin doka. A wata takarda da ta aike wa manema labarai a yau Litinin da ke ɗauke da sanya hannun Sheikh Ibrahim Shehu Maihula, wato Mataimakin Shugaban Majalisar Shura ta Tijjaniya, ɗariƙar ta ce ta shiga halin tilas ne na yin magana akan al'amarin musamman ganin yadda aka cigaba da tsare shehin malamin, wanda ya shafe tsawon kusan watanni…
Read More

Harin baƙin haure: ‘Yan Nijeriya sun yi tir da shawarar Gwamnatin Tarayya ta kulle a Afirka ta Kudu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja 'Yan Nijeriya mazauna Afirka ta Kudu sun koka game da abin da suka kira da sakaci daga ɓangaren Gwamnatin Tarayya akan abin da ya shafi lamuransu tare kira a gare ta da ta ɗauki matakan kare rayukansu da dukiyoyinsu sakamakon ƙarin zanga-zangar ƙin baƙi da ke ƙara ta’azzara a ƙasar. Hukumar kula da lamuran ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje NiDCOM, ta bada umarnin rufe shaguna na ɗan lokaci tare da shawartar mutane su zauna a gidajensu na ɗan lokaci sakamakon fargabar ɓarkewar tashin-tashina. An ruwaito cewa, wata zanga-zangada aka fara ta rikiɗa zuwa tashin…
Read More

‘Yan bindiga sun sace yara 23 a gidan marayu da matar mai wajen

Wasu da ake zargin 'yan bindiga sun yi awon-gaba da ɗalibai guda 23 tare da matar mamallakin makarantar Dahallukitab Group of School da ke Zariagi, kusa da mahaɗar Kabba a kan hanyar Lokoja zuwa Okene, a ƙaramar hukumar Adavi ta jihar Kogi. Daily Trust ta rawaito cewa harin ya faru ne a daren Lahadi, inda maharan su ka kutsa cikin harabar makarantar wacce kuma ke matsayin gidan marayu, suna harbe-harbe a iska kafin su yi awon gaba da yaran zuwa wani wuri da ba a sani ba. Mazauna yankin sun ce lamarin ya fara ne da misalin ƙarfe 10:30 na…
Read More

Kotu ta haramta wa ‘yan jarida ɗaukar shari’ar waɗanda ake zargi da yunƙurin juyin mulki

Alƙalin Babbar Kotun Tarayya a Abuja, Joyce Abdulmalik, ta hana ‘yan jarida shiga da kuma ɗaukar rahotan shari’ar wasu mutane shida da ake zargi da shirya juyin mulki. Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan jarida sun isa kotun da sassafe domin bibiyar shari’ar, amma kafin fara zama, jami’an kotu suka umarce su da su fice bisa umarnin alƙaliyar. Duk da ƙorafin da suka yi cewa shari’ar na da muhimmanci ga jama’a, jami’an sun nace cewa umarni ne daga kotu. Bayan fitar da ‘yan jaridar, an kulle ƙofar kotun, inda daga bisani Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya, Lateef Fagbemi, ya…
Read More

Sakataren APC na Ƙasa ya soki Atiku kan barci a taron Ibadan

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babban Sakataren jam’iyyar APC na Ƙasa, Ajibola Basiru, ya yi tsokani tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar bayan wani hoto da ya nuna yana barci a taron jam’iyyun adawa da aka gudanar a Ibadan, Babban Birnin Jihar Oyo. Ajibola Basiru ya wallafa hoton a shafinsa na Facebooka yau Lahadi, inda ya cewa: "Jagoran adawa ya yi barci a wannan muhimmin taron na jam’iyyun adawa." Hoton, wanda aka ɗauko daga gidan talabijin na Arise News, ya nuna Atiku Abubakar yana zaune kusa da Kabiru Turaki, shugaban tsagi na jam’iyyar PDP, a yayin taron. Wallafa hoton…
Read More

Trump ya magantu bayan tsallake rijiya da baya yayin harin bindiga

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Donald Trump na Amurka ya magantu bayan wani al'amarin firgici ya auku a kusa da Fadar White, inda ya bayyana halin da ya tsinci kansa aciki a matsayin "aiki mafi wahala", bayan faruwar abin da hukumomi suka kira da yunƙurin kisan kai da gangan. Da yake jawabi a wani taron manema labarai sa'o'i bayan faruwar al'amarin, Trump ya bayyana cewa wani da ake zargi ɗan bindiga ne ya kutsa wa shingen binciken jami'an tsaro kana daga bisani jami'an leƙen asirin ƙasar suka daƙile harin nasa. Rahotanni sun bayyana cewa, gaggauta fitar da Trump…
Read More

An kama wanda ake zargi da harbe-harbe a taron cin abincin dare na wakilan Fadar White House

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An hanzarta fitar da Shugaba Donald Trump daga dandamali yayin da aka ƙaddamar da wasu harbe-harbe a taron cin abincin wakilan Fadar White House. Trump ya ce, wani da ake zargin ɗan bindiga ne da makamai da dama ya kutsa wa shingen binciken jami'an tsaro kana ya fara harbe-harbe a wajen taron. An ruwaito cewa, an ɗauke Trump da sauran jami'an gwamnati da ke wajen cikin aminci. Sannan, wanda ake zargin, wanda a yanzu yake hannun hukuma, za a gurfanar da shi bisa tuhumar sa da laifin amfani da bindiga yayin tarzoma da kuma…
Read More

Trump ya tsallake rijiya da baya yayin farmakin bindiga a Fadar White House

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An gaggauta fitar da Shugaba Donald Trump na Amurka da Matarsa, Melania Trump daga wajen taron cin abincin dare na shekara-shekara na wakilan Fadar White House da aka saba yi a Birnin Washington D.C a ranar Asabar a lokacin da wani ɗan bindiga ya buɗe wuta ana tsaka da shagali. Al'amarin ya faru ne a daidai wajen da jami'an tsaro ke tantance mahalarta, inda mutumin ya yi yunƙurin kutsawa tare da buɗe wa jama'ar wajen wuta. Haka kuma, wani jami'in sirri ya tsallake rijiya da baya bayan harbinsa da aka yi a lokacin da…
Read More

Taron Ibadan: Jam’iyyun adawa sun zaɓi fitar da ɗan takara ɗaya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɓangaren adawa a siyasar Nijeriya na shirin ɗaukar wani salo yayin da a ranar Asabar haɗakar 'ya'yan jam'iyyu suka cimma matsayar ajiye bambance-bambancen da ke tsakanin da tsayar da ɗan takara ɗaya da zai ƙalubalanci jam'iyya mai mulki (APC) a babban zaɓen 2027. Rahotanni sun bayyana cewa, wasu manyan ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar da dan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 na jam’iyyar LP, Peter Obi da wasu manyan ‘yan siyasa na goyon bayan ra’ayin kafa gamayyar jam’iyyun adawa a Nijeriya. Ana ganin wannan…
Read More