29
Apr
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da goyon baya tsohon Kwamishinan Ayyuka, Mustapha Gubio don tsaya wa takarar gwamna a jihar, yayin babban zaɓen 2027. Malam Dauda Iliya, wato Mai ba gwamnan shawara akan harkokin yada labarai ya tabbatar da haka ga NewsPointNigeria, jim-kaɗan bayan karɓar baƙuncin Gubio, wanda ya mallaki fom ɗin tsayawa takara a Abuja. A wannan ci-gaba, an ga yadda hotunan da mai ba gwamnan shawara ya yaɗa suna nuna Mustapha Gubio na gabatar da fom ɗin nasa ga Gwamna Zulum. Wannan goyon baya ta haifar da cece-kuce a…
