Babaji

5684 Posts

Amurka za ta janye sojoji 5,000 daga Jamus – Jami’ai

Amurka na shirin janye sojojinta kusan guda 5,000 daga Jamus, a daidai lokacin da taƙaddama ke ƙaruwa tsakanin ƙasashen biyu akan batun yaƙin Iran, kamar yadda rahotanni suka bayyana. Shugaba Donald Trump ya zargi ƙawayen Turai da rashin nuna cikakken goyon baya ga yaƙin, lamarin da ya janyo rashin jituwar difulomasiyya a tsakaninsu. A nasa ɓangaren, Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya zargi Amurka da fuskantar ƙasƙanci daga Iran yayin da ake tattaunawa domin kawo ƙarshen rikicin. Rahoton ya ce, ana sa ran janyewar sojojin za ta gudana ne cikin watanni shida zuwa goma sha biyu masu zuwa. Kamfanin dillancin…
Read More

JAMB za ta sanya adadin makin samun gurbin karatu a manyan makarantu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makaranta (JAMB), ta sanar da cewa za ta gudanar da taron manufofin shiga jami’o’i na shekarar 2026 a ranar 11 ga Mayu, 2026 a Abuja. JAMB ta ce, za ta yi hakan ne domin tantance mafi ƙarancin makin UTME (cut-off mark) da kuma sabbin ƙa’idojin shiga manyan makarantu a faɗin ƙasar. A wata sanarwa da Kakakin JAMB, Fabian Benjamin, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce taron zai haɗa da manyan masu ruwa da tsaki a fannin ilimi, inda Ministan Ilimi, Tunji Alausa, zai bayyana muhimman sababbin tsare-tsare da…
Read More

Obi da Kwankwaso sun koma NDC a hukumance

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon gwamnan Jihar Anambara, Peter Obi kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyya LP a zaɓen 2023 da tsohon gwamnan Jihar Kano, Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso, sun shiga jam’iyyar NDC, wato National Democratic Congress NDC a hukumance. Manyan ‘yan siyasar biyu sun kammala ɗaukar wannan mataki ne a ranar Lahadi bayan ganawa da jagoran jam’iyyar kuma tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Seriake Dickson a Abuja, inda suka sanar da sauyin tafiyarsu zuwa sabuwar jam’iyyar adawa yayin tunkarar babban zaɓen 2027. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da ganin sauye-sauyen…
Read More

NAHCON ta fara jigilar Hajjin 2026 da maniyyata 474 daga Jihar Kogi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON), ta ƙaddamar da jigilar Hajjin 2026 da jirgin farko daga Abuja, inda aka ɗauki maniyyata 474 daga Jihar Kogi zuwa ƙasar Saudiyya. An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne a Abuja bayan sauya shirin farko da aka yi na tashi daga Jihar Ogun. Shugaban NAHCON, Ambasada Isma’il Abba Yusuf, ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima bisa goyon bayan da suke bayarwa wajen tafiyar da harkokin hukumar bisa tsari. Ya kuma buƙaci maniyyata da su bi dukkan ƙa’idoji musamman amfani da katin Nusuk, tare da tabbatar da…
Read More

Tinubu ya naɗa Bianca Ojukwu a matsayin ministar harkokin waje

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Bianca Ojukwu a mtsayin babbar minister harkokin waje. Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa daga kakakin shugaban Bayo Onanuga da ta tabbatar da nadin uwargidan marigayi madugun ‘yan awaren Biyafara da a ka yi wa ahuwa Odumegwu Ojukwu. Dama Bianca Ojukwu ce karamar minista ma’aikatar gabanin daga darajar mukaminta da ya biyo bayan murabus din tsohon ministan ma’aikatan Yusuf Tuggar wanda ya tafi Bauchi don shiga takarar gwamna. Kazalika shugaban ya kawo sunan Sola Enikanolaiye don zama karamin ministan harkokin wajen. Enikanolaiye dai daga jihar Kogi ya…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta ayyana 1 ga Mayu a matsayin hutu ga Ranar Ma’aikata

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta ayyana Juma'a, 1 ga watan Mayu, 2026 a matsayin rana hutu domin karrama Ranar Ma'aikata ta duniya ta 2026. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya sanar da haka a madadin gwamnatin, a wata sanarwa da Babbar Sakatariyar a ma'aikatar, Dakta Magdalene Ajani ta fitar a ranar Laraba. Da ya ke taya ma'aikata murnar zagayowar ranar ta bana, ministan ya yaba wa ma'aikatan Nijeriya bisa jajircewa da sadaukarwarsu wajen samar da ci-gaba a ƙasa. Tunji Ojo ya kuma buƙaci ma'aikatan da su zama masu kishin ƙasa, ƙwazo da sadaukar da…
Read More

Tinubu ya tsige Shugaban NMDPRA bayan wata huɗu da naɗa shi

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kori Mista Saidu Mohammed, Babban Jami'in Gudanarwa na Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA). An sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai magana da yawun shugaban ƙasa, ya fitar a ranar Laraba. Onanuga, wanda ya sanar da cewa Mista Rabiu Abdullahi Umar zai maye gurbinsa, ya ce korar Saidu Mohammed ya dace da "maslahar al'umma." Sanarwar ta kuma nuna cewa nadin Abdullahi Umar a matsayin sabon Babban Jami'in Gudanarwa na NMDPRA yana ƙarƙashin tabbatarwar Majalisar Dattawa. Onanuga ya ce canjin shugabanci, wanda aka yi bisa ga Dokar Masana'antar…
Read More

2027: Zulum ya goyi bayan tsohon kwamishina, Gubio don tsaya wa takarar gwamnan Borno

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da goyon baya tsohon Kwamishinan Ayyuka, Mustapha Gubio don tsaya wa takarar gwamna a jihar, yayin babban zaɓen 2027. Malam Dauda Iliya, wato Mai ba gwamnan shawara akan harkokin yada labarai ya tabbatar da haka ga NewsPointNigeria, jim-kaɗan bayan karɓar baƙuncin Gubio, wanda ya mallaki fom ɗin tsayawa takara a Abuja. A wannan ci-gaba, an ga yadda hotunan da mai ba gwamnan shawara ya yaɗa suna nuna Mustapha Gubio na gabatar da fom ɗin nasa ga Gwamna Zulum. Wannan goyon baya ta haifar da cece-kuce a…
Read More

Tinubu ya ba jakadun Nijeriya filaye a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ministan Birnin Tarayya Abuja Nyesom Wike, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya amince da wani muhimmin shiri na bai wa jakadu da manyan jami’an difulomasiyya filaye a birnin don ƙarfafa hulɗar ƙasa da ƙasa da kuma bunƙasa tattalin arzikin ƙasa. Wike ya bayyana cewa wannan mataki ba wai kawai don kyautata zamantakewar jakadun ba ne, har ma wata dabara ce ta ƙara kusantar Najeriya da ƙasashen waje ta fuskar diflomasiyya. A cewarsa, idan jakadu sun samu kyakkyawan muhalli da damar gudanar da ayyukansu cikin sauƙi, hakan zai ƙara inganta hulɗa tsakanin Najeriya da ƙasashen…
Read More

Kotu ta haramta wa INEC karɓar tarukan ADC na jihohi

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta hana Hukumar Zaɓe INEC, amincewa ko shiga dukkan wani taro na jam’iyyar ADC da wani shugabanci riƙon ƙwarya da take ƙoƙarin gudanarwa. Jaridar PUNCH ta rawaito cewa a hukuncin da Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta yanke, kotun ta kuma haramta wa tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, da wasu jiga-jigan jam’iyyar tsoma baki cikin ayyukan shugabannin jihohi da aka zaba. Shari’ar ta samo asali ne daga karar da Norman Obinna da wasu shida suka shigar a madadin shugabannin jihohin jam’iyyar, inda suka kalubalanci halaccin kwamitin rikon kwarya da kuma yunkurinsa na shirya tarukan…
Read More