Babaji

5684 Posts

A ƙarshe, Ganduje ya kira da Sanusi a matsayin Sarkin Kano

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Talata tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana amincewa da Alhaji Muhammadu Sanusi na II a matsayin Sarkin Kano kuma Shugaban majalisar sarakunan Kano. Ganduje ya bayyana haka ne yayin taron rantsar da sabon mataimakin gwamnan jihar Kano, Murtala Sule Garo a Gidan Gwamnatin jihar.. A yayin jawabinsa, tsohon gwamnan ya yi gaisuwa ga Sanusi da kiran sa da cikakken sunan sarauta, lamarin da mahalarta taron suka yaba wa. Wannan shi ne karo na farko da Ganduje ya bayyana a fili ɗaukar Sanusi a matsayin sahihin wanda ke riƙe da…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Karon farko cikin shekaru 20, Arsenal ta kai wasan ƙarshe a Champions League

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta tsallake zuwa zangon wasan ƙarshe na gasar Zakarun Nahiyar Turai, wato UEFA Champions League, bayan doke Atletico Madrid da ci 1 da nema a wasan dab da na ƙarshe na biyu. An tashi wasan farko ne 1 da 1 a gidan Atletico Madrid a makon da ya gabata. Wannan na nufin Arsenal za ta haɗu Paris Saint Germain ko kuma Bayern Munich a wasan na ƙarshe domin neman lashe kofin na 2026. A shekarar 2006 ne Arsenal ta kai wasan ƙarshe a gasar, inda a lokacin ne ta…
Read More

Kotu ta umarci SERAP ta biya diyyar miliyan N100 ga jami’an DSS kan ɓatanci

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta umarci ƙungiyar kula da tabbatar da gaskiya da adalci ga 'yancin al'umma (SERAP) ta biya jami’an DSS biyu diyyar Naira miliyan 100 bisa zargin ta da ɓata suna. Haka kuma, kotun ta umarci SERAP da ta biya Naira miliyan 1 a matsayin kuɗin shari’a, tare da wallafa neman afuwa ga jami’an a shafinta na X da kuma a jaridu da gidajen talabijin na ƙasa. Hukuncin ya biyo bayan wata sanarwa ne da SERAP ta fitar a shekarar 2024, inda ta zargi jami’an DSS da kai samame ba…
Read More

Wajibi ne yankunan Abuja da Kaduna su ba jiragen ƙasa da kayayyakinsu kariya – NRC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar kula da jiragen ƙasa ta Ƙasa (NRC) ta yi kira ga yankunan da ke kusa da layin dogo na Abuja zuwa Kaduna da su ba jirage da kayayyakinsu kariya daga hare-hare da lalata su da ke cigaba da faruwa a kisa da su. Wannan na zuwa ne a daidai da ayyukan ɓata-gari da lalata kayayyakin suka yawaita, lamarin da NRC ta yi alla-wadai da shi da babbar murya musamman ganin yadda ɓata-garin suke cin karensu babu babbaka a layin dogon. A cewar NRC, al'amarin na kwanan nan ya faru ne daga kilomita 177…
Read More

WPFD: Wajibi ne kafafen labarai da gwamnatoci su haɗa kai don magance labarai masu ruɗarwa – Idris

Gwamnatin Tarayya ta nemi kafafen yaɗa labarai, hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki su ƙara haɗa kai domin magance yaduwar labaran karya da na bata-gari, tana mai jaddada cewa hakan na da matukar muhimmanci wajen kare amincewar jama’a da kuma zaman lafiyar kasa. Ministan Yada Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin bikin Ranar Ƴan Jarida ta Duniya ta shekarar 2026 da aka gudanar a Radio House. Ya ce, gwamnati na da ƙudiri wajen kare 'yancin 'yan jarida kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, tare da samar da yanayi mai kyau…
Read More

DA ƊUMI-ƊUMI: Kwana ɗaya bayan komawar Obi da Kwankwaso NDC an maka jam’iyyar a kotu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sa'o'i bayan tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi da tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso sun shiga jam'iyyar NDC a hukumance, an sabon rikici akan zargin ta da rashin kiyaye sharuɗɗan rajista daga Hukumar Zaɓe, INEC. Hakan na zuwa ne a lokacin da jagoran jam'iyyar ADA, Umar Ardo ya ƙalubalanci sahihancin rajistar NDC a kotu, inda ya zargi jam'iyyar da gaza cika sharuɗɗan dokokin ƙasa da tsare-tsaren kafin amincewa da ita a hukumance. An samu wannan al'amari ne jim-kaɗan bayan shigar Obi da Kwankwaso cikin NDC a hukumance, inda aka na su…
Read More

Ɓangaren Gwamna Makinde ya naɗa Kabiru Turaki a matsayin shugaban riƙo na PDP

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɓangaren jam’iyyar PDP da ke goyon bayan Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya sanar da naɗa Kabiru Tanimu Turaki a matsayin shugaban riƙon ƙwarya na ƙasa na jam'iyyar. An naɗa Turaki ne domin jagorantar kwamitin riƙo mai mambobi 13 a ranar Litinin, yayin taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) karo na 103 da aka gudanar a Abuja, kamar yadda rahotanni suka bayyana. Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin shugabanci ke addabar jam’iyyar a mataki na ƙasa.
Read More

Rikicin APC a Gombe ya yi ƙamari yayin da Gwamna Inuwa da Sanata Goje ke kafsawa kan tikitin sanata

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An samu sabon rikicin siyasa acikin jam'iyyar APC a Jihar Gombe yayin da Gwamna Inuwa Yahaya da magoya bayan tsohon gwamnan jihar kuma sanata a yanzu, Ɗanjuma Goje suka bayyana muradin yankar tikitin sanatar Gombe ta Tsakiya a zaɓen 2027. Wannan al'amari ya samo asali ne a lokacin da aka ayyana Mohammed Ahmadu Deba a matsayin ɗan takarar kujerar sanata a mazaɓar a matakin yarjejeniyar 'ya'yan jam'iyya, lamarin da zai ba shi damar maye gurbin Sanata Goje, wanda ya haifar da ɓaraka a tsakanin masu biyayya ga Gojen. Masu biyayyan na ganin wannan mataki…
Read More

Kano: An yi wa yara 112,005 rigakafin foliyo a Bichi

Aƙalla yara dubu ɗari da goma sha biyu da biyar 'yan ƙasa da shekaru biyar ne, suka amfana da allurar rigakafin cutar shan-inna a Ƙaramar Hukumar Bichi da ke Jihar Kano. Kamar yadda Jami'ar Yaɗa Labarai ta yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta rawaito, Wakilin Hukumar Lafiya ta Duniya, Malam Zakari Sani ne ya bayyana hakan a yayin taron tattauna yadda aikin rigakafin ya kansance a ƙaramar hukumar. Zakari Sani, ya kuma tabbatar da gagarumar nasarar da yankin ya samu dangane da wasu ma'aunai da jiha ke auna ƙoƙarin kowace ƙaramar hukuma wajen gudanar da aikin rigakafin, wanda Ƙaramar Hukumar…
Read More

Gwamnatin Kano za ta riƙa kashe Dala ɗaya a wata ga kowane yaro don inganta lafiya

Gwamnatin Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf, ta ɗauki nauyin kashe Dala ɗaya, wato kimanin Naira 1,500, ga kowane yara da ke faɗin jihar, domin inganta lafiya da kuzarinsu, ta hanyar haɗin gwiwa da Ƙungiyar (ICSA) mai taken Haɗaɗɗan Shirin Tallafa Wa Lafiyar Ƙananan Yara. A sanawar da Jami'ar Yaɗa Labarai ta Ƙaramar Hukumar Bichi, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta fitar, a yayin da ƙungiyar ta kai ziyara ƙaramar hukumar, da yake gudanar da jawabi, wakilin Kungiyar Lafiya ta Duniya na karamar hukumar, Malam Zakari Haruna, ya bayyana kwamitocin da aka kafa a dukkan ƙananan hukumomi 44 na…
Read More