Babaji

5687 Posts

APC ta sauya lokutan fidda gwani na shugaban ƙasa da gwamnoni

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam’iyya mai mulki APC, ta sanar da ɗage zaɓukan fidda gwani na shugabancin ƙasa da gwamnoni, tare da fitar da sabon jaddawalin gudanar da su. A sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis, ta ce an ɗage zaɓukan ne domin bai wa jam’iyya damar kammala shirye-shirye da gyare-gyare kafin gudanar da su cikin tsari mai kyau. Jaddawalin ya nuna cewa za a fara sayar da fom daga ranar 28 ga Afrilu, 2026, sannan a rufe sayar da fom a ranar 10 ga Mayu, 2026. Za a gudanar da ayyukan tantance ’yan takara daga ranar…
Read More

Gwamnan Zamfara ya gana da Tinubu akan tsaro, tattali da zaɓen 2027 a Abuja

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Alhamis, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda suka tattauna muhimman batutuwan da suka shafi tsaro, tattalin arziƙi da kuma siyasar shekarar 2027. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa ganawar ta fi karkata ne kan halin tsaro a Zamfara, bunƙasar tattalin arziƙi, da kuma al’amuran siyasa da ke tafe. Sanarwar ta nuna cewa, shugaban ƙasar ya sake jaddada ƙudirin Gwamnatin Yarayya na ƙara yawan sojoji da kuma samar da kayan aiki domin tabbatar…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: DSS ta gurfanar da El-Rufa’i kan naɗar hirar Ribaɗu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, ta gurfanar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai a gaban Mai Shari'a Joyce Abdulmalik ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa zargin sa da naɗar hirar wayar tarho ba bisa doka ba. Rahotanni sun bayyana cewa, an ɗauki matakin ne sakamakon zargin da ake yi wa El-Rufa'i na hannu a naɗar hirar Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro, Nuhu Ribaɗu. Wannan tuhuma na ɗaya daga cikin waɗanda hukumar ta shigar akan sa tun a watan Fabrairu a ƙara mai lamba kamar haka FHC/ABJ/CR/99/2026,…
Read More

Majalisar Dokokin Kano ta kafa kwamiti don tantance Murtala Garo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Majalisar Dokokin Jihar Kano ta kafa wani kwamitin wucin gadi domin tantance Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamnan jihar. An ɗauki matakin ne bayan karanta wasiƙar da Abba Kabir Yusuf ya aike wa Shugaban majalisar Jibril Ismail Falgore, a zaman majalisar na ranar Laraba. Gwamnan ya bayyana cewa ya zaɓi Garo ne bayan tuntuba mai zurfi, yana mai cewa gogaggen ɗan siyasa ne da ya riƙe muƙamai daban-daban, ciki har da shugaban ƙaramar hukuma, shugaban ALGON a jihar, da kuma kwamishina. Shugaban majalisar ya sanar da kafa kwamitin ƙarƙashin jagorancin manyan shugabannin majalisar…
Read More

Jakadan Nijeriya a Aljeriya, Mahmud Lele ya rasu bayan shekaru 50 a duniya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mohammed Mahmud Lele, wanda shi ne jakadan Nijeriya da aka naɗa zuwa ƙasar Aljeriya, ya rasu bayan shafe shekaru 50 a duniya, kamar yadda rahotanni da dama suka bayyana. Ma’aikatar Harkokin Waje ta bakin Kakakinta, Kimiebi Ebienfa ta sanar da haka inda ta ce marigayin ya rasu ne a birnin Ankara na ƙasar Turkiyya a ranar 19 ga Afrilu, 2026 bayan fama da jinyar rashin lafiya na tsawon lokaci. Ta kuma bayyana mutuwarsa a matsayin babban rashi ga makusantansa da ma Nijeriya baki ɗaya. Gabanin rasuwar marigayin, an naɗa shi domin wakiltar Nijeriya a…
Read More

Kotu ta umarci a tsare waɗanda ake zargi da kitsa juyin mulki a komar DSS

Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta bayar da umarnin tsare wasu mutane shida da ake zargi da hannu a kitsa juyin mulki a hannun Hukumar Tsaro ta Farin kaya Kaya (DSS), bayan an gurfanar da su akan tuhume-tuhume guda 13 da suka shafi zargin ta’addanci. A zaman kotun da aka fara da misalin ƙarfe 1:46 na rana a ranar Laraba, Babban Lauyan tarayya, Lateef Fagbemi (SAN), ya shaida wa kotun cewa an shirya tuhumar, inda ya nemi a karanta wa waɗanda ake zargin laifukan da ake tuhumarsu da su. Sai dai shari’ar ta ɗan tsaya na ɗan lokaci bayan wanda…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Bayo Adelabu ya sauka a ministan lantarki don tsaya wa takarar gwamnan Oyo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, ya yi murabus daga muƙaminsa domin neman takarar gwamna a jihar Oyo a yayin zaɓen 2027. A wasiƙar murabus ɗin da ya fitar mai kwanan wata 22 ga Afrilu, 2026, wadda ya aike wa Shugaba Bola Tinubu, Adelabu ya bayyana cewa wannan mataki zai fara aiki ne daga ranar 30 ga watan Afrilu, 2026, domin bada sararin miƙa ragamar yadda ya dace. Ya bayyana cewa ya sauka ne tare da matuƙar girmamawa da godiya ga Shugaba Bola Tinubu da ya naɗa shi a muƙamin. “Na rubuta wannan wasiƙa ne tare…
Read More

Kamar PDP, Kotun Ƙoli ta jingine hukuncin shari’ar rikicin shugabancin ADC

A yau Laraba Kotun Ƙoli a ta sanar da ɗage yin hukunci akan ƙarar da David Mark, shugaban tsagin jam’iyyar ADC ya shigar akan Nafiu Bala, tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa. Mai Shari'a Lawal Garba, wanda ke jagorantar kwamitin alƙalai guda biyar, ya bayyana hakan ne bayan lauyoyin bangarorin biyu sun gabatar da hujjojinsu a gaban kotu. Ya bayyana cewa, za a sanar da ranar da za a yanke hukuncin daga baya ga dukkan ɓangarorin da ke shari’ar. Mark ya roƙi kotun da ta dakatar da aiwatar da hukuncin Kotun Daukaka Kara na ranar 12 ga watan Maris, wanda…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Chelsea ta tsige Liam Rosenior bayan shan kaye sau biyar a jere

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta sallami Liam Rosenior daga matsayin kocin bayan rashin nasara a wasanni biyar na Premier League ba tare da zura kwallo ko daya ba. Follow Muje wasanni Shugabannin kungiyar sun hadu bayan shan kashi da Brighton kuma an yanke shawarar cewa canji nan take ya zama dole domin kokarin ceton kakar wasa da kuma tunkarar wasan kusa da na karshe na Kofin FA da Leeds ke gaba. Ƙungiyar ta ce, “Liam koyaushe yana gudanar da kansa tare da cikakkiyar gaskiya da kwarewa tun bayan nadin sa a tsakiyar kakar. Wannan ba wani yanke shawara ba…
Read More

Yanzu-yanzu: Tinubu na ganawa da Jonathan a Fadar Shugaban Ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yau Laraba ne Shugaba Bola Tinubu ya karɓi baƙuncin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. Saidai babu wani cikakken bayani a game da abin da ganawar tasu ta ƙunsa a yayin haɗa wannan rahoto. Jonathan dai shi ne shugaban Nijeriya daga shekarar 2010 zuwa 2015. Sunansa ya ƙara ƙarfi ne a 2015 a lokacin da ya karɓi kaye a zaɓen shugaban ƙasa da tsohon shugaban ƙasa marigayi Muhammadu Buhari ya doke shi a kai, lamarin da kuma ya sa ya zama shugaban Nijeriya na farko da…
Read More