22
Apr
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya zaɓi Alhaji Murtala Sule Garo a matsayin sabon mataimakin gwamna bayan saukar Kwamared Abdulsalam Gwarzo a muƙamin. Rahotanni sun bayyana cewa, Abdulsalam Gwarzo ya yi murabus ne bayan ɓarkewar rikici tsakaninsa da gwamnan a lokacin da ya (Abba) fice daga jam'iyyar NNPP ya koma APC mai mulki. Wannan al'amari ya haifar da tsama a dangantakar aiki ta mutanen biyu, inda tsohon mataimakin gwamnan ya shiga halin matsi na ya bi gwamnan amma kuma ya tirje akan ƙin amince wa hakan. Akan ƙamarin rikicin nasu ne majalisar…
