Babaji

5687 Posts

Boko Haram ta ba gwamnati kwana uku na amsa buƙatunta ko ta halaka mutane 416 da ta sace

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mayaƙan Boko Haram sun sake jefa fargaba acikin al'umma a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya yayin da suka ba wa hukumomi wa'adin kwanaki uku na makomar mutane guda 416 da suka sace, yayin da suke gargaɗi akan yunƙurin ceto su da ƙarfi. A wani faifan bidiyo da mayaƙan ƙungiyar suka fitar a safiyar ranar Litinin, ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa matuƙar aka gaza biyan buƙatun zuwa lokacin da ta bayar, za ta kai mata da yaran zuwa wasu ɓoyayyun wurare da ba za a sake ganin su ba. 'Yan ta'addan, waɗanda suka yi shiga…
Read More

Tsofaffin ‘yan sanda sun yi cincirindo a mashigar Fadar Shugaban Ƙasa kan tsarin fansho

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yau Litinin ne wasu tsofaffin jami’an rundunar ’yan sanda da suka gudanar da zanga-zanga a yankin Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda suka nemi Shugaba Bola Tinubu da ya sanya hannu akan fara amfani da dokar barin aiki na 'yan sanda, wanda Majalisar Dattawa ta kammala aiki a kai tun a watan Disambar 2025. Rahotanni sun bayyana cewa, ƙudirin na neman fitar da rundunar 'yan sanda daga tsarin fansho na 'Contributory Pension Scheme'.. An ga yadda masu zanga-zangar ɗauke alluna masu rubutu suka tun daga yankin rassan gwamnati uku zuwa yankin hedikwatar…
Read More

An yi jana’izar tsohon Shugaban NFF, Ibrahim Galadima a Kano

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A jiya Lahadi aka yi jana'izar marigayi Ibrahim Galadima, tsohon Shugaban Hukumar Ƙwallon ƙafa ta Ƙasa (NFF), a Masallacin Juma'a na Fagge da ke Kano. Taron jana'izar ya samu halartar masu alfarma daga sassa daban-daban na Nijeriya. Daga cikinsu akwai Mai Martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, Shugaban Hukumar Wasanni ta Ƙasa, Alhaji Shehu Dikko, Shugaban NFF, Alhaji Ibrahim Musa Gusau da kuma tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau. Tuni dai Ƙungiyar Maruwaita Labaran Wasanni ta Ƙasa (SWAN) ta aike da saƙon ta'aziyyarta ga iyalan marigayin bisa rasuwarsa bayan fama da…
Read More

Sojoji sun kama sama da mutum 20 bisa zargin ta’addanci cikin sa’o’i 24

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar Sojojin Nijeriya ta kama sama da waɗanda ake zargi da ta'addanci guda 20 a wani atisaye na musamman da jami’anta suka gudanar a sassan daban-daban na ƙasar yayin sabunta yaƙi da ta'addanci. A cewar wani rahoton aiki da rundunar ta fitar a ranar Lahadi ga manema labarai a Abuja, an yi kamen ne yayin wani atisaye da ya ƙunshi dakarunta da sauran jami'an wasu hukumomin tsaro da kuma haɗin-gwiwar ƙungiyoyin 'yan bijilante, inda suka hari maɓoyar 'yan ta'adda da suka haɗa da masu garkuwa da mutane da masu aikata sauran manyan laifuka a…
Read More

Harry Kane ya zura ƙwallaye 32 yayin da Bayern ta lashe Bundesliga ana saura wasa huɗu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Bayern Munich ta lashe gasar Bundesliga a karo na 35 a ranar Lahadi bayan doke VFB Stuttgart da ci 4 da 2. Wannan na nufin Bayern ta lashe kofin tun ana sauran wasanni huɗu a ƙarƙare gasar na wannan kakar. Haka kuma, ƙungiyar ta zura jimillar ƙwallaye 109 zuwa yanzu, inda ta yi rashin nasara a wasa ɗaya kachal yayin haka. Ɗan wasan gaba na ƙungiyar, Harry Kane ya zura jimillar ƙwallaye 32, wanda ke ƙara nuna ƙwarewarsa wajen zura ƙwallo a ragar abokan karawa. A yanzu dai ƙungiyar tana harin lashe kofin…
Read More

Malaman makaranta a Abuja sun fara yajin aiki

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Malaman makarantun sakandare da framare na gwamnati a Birnin Tarayya Abuja sun shirya fara zanga-zanga a yau Litinin, bayan wani umarni daga majalisar zartarwar (SWEC) Ƙungiyar Malamai ta Ƙasa. An fitar da umarnin ne bayan wani zaman gaggawa da aka gudanar a Gwagwalada, Abuja a ranar Juma'a. Shugaban reshen birnin, Abdullahi Shafa; Sakatariya, Margaret Jethro; da Sakataren yaɗa labarai, Ibukun Adekeye ne suka fitar da sanarwar. A ciki, ƙungiyar ta umarci dukkan malamai da su janye daga gudanar da ayyukansu da jiran umarni na gaba akan al'amarin. Haka kuma, an shawarci iyaye da su…
Read More

Manchester City ta rage tazarar tsakaninta da Arsenal zuwa maki uku bayan doke ta da ci 2 da 1

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gasar Premier League na ƙasar Ingila ya sake ɗaukar wani salo bayan da ƙungiyar Manchester City ta doke Arsenal da ke kan teburin gasar da ci 2 da 1 filin wasa na Etihad. Wannan sakamako ya rage tazarar da Arsenal ta ba City a teburin gasar zuwa maki uku yayin da ita kuma Cityn take da wasa ɗaya a hannu. Ɗan wasa Rayan Cherki ne ya fara zura ƙwallo a ragar Arsenal a minti na 16, inda bayan mintina biyu murnar magoya bayan City ta koma ciki a lokacin da Kai Havertz ya farke…
Read More

JAMB ta fitar da sakamakon jarrabawar UTME da aka yi a Juma’a da Asabar

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar haɗaka ta kula da lamuran samar da gurbin karatu a manyan makarantu ga ɗalibai (JAMB), ta fitar da sakamakon ɗaliban da suka rubuta jarrabawar UTME a ranakun 17 da 18 ga watan Afrilu. A wata sanarwa da Kakakin JAMB, Fabian Benjamin ya fitar wa manema labarai a yau Lahadi, hukumar ta bayyana cewa sakamakon ɗalibai guda 1,264,940 ne da suka rubuta a kwana biyun aka sako. Haka kuma, hukumar ta tunatar da cewa ta fitar da wanda aka yi a ranar Alhamis. Da fari, JAMB ta fitar da sakamakon ɗalibai 632,752 da suka…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Shekarau ya koma APC daga PDP

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau ya koma jam'iyyar APC a hukumance bayan shafe makonni na shawarwari da kuma yawaitar jita-jitar sauya alƙiblar siyasarsa. Rahotanni sun bayyana cewa, Shekarau ya koma APC ne tare da Sanata Bello Hayatu Gwarzo, wanda shi ma jigo ne a PDP, lamarin da ke nuna an samu gagarumin sauyi a fagen siyasar Kano. Sanannun 'yan siyasar biyu sun sanar da haka ne a yau Lahadi a gidan Shekarau da aka fi sani da Fadar Munduɓawa a Kano, inda masu biyayya da magoya baya da dama suka halarta. Da yake…
Read More

Gwamnan Bauchi ya soke shirin koma wa APC kan rashin cimma yarjejeniyar 60-40

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam'iyyar PDP a Jihar Bauchi ta kawo ƙarshen tattaunawa da jam'iyya mai mulki (APC) a hukumance bayan da ɓangarorin biyu suka gaza cimma yarjejeniya akan sharuɗɗan da ake buƙata na sauya salon siyasar gwamnatin jihar. Shugaban PDP a jihar, Sama'ila Burga ya bayyana haka a yau Asabar yayin hira da manema labarai a sakatariyar jam’iyyar da ke cikin garin Bauchi. Ya bayyana cewa, bayan tattaunawa tsakanin Gwamna Bala Mohammed da wasu jami'an jam'iyyar, da kuma a matakin ƙasa da ya haɗa Mataimakin Shugaban ƙasa, Kakakin Majalisar Wakilai da wasu tsofaffin gwamnoni guda uku, APC…
Read More