Babaji

5689 Posts

Shettima ya ziyarci waɗanda harin boma-boman Maiduguri ya shafa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya jaddada matakin Gwamnatin Tarayya na kawo ƙarshen ta'addanci a Nijeriya, yana mai cewa waɗanda suke da hannu a hare-haren kwanan nan za su fuskanci hukuncin doka. Shettima ya ce, baya ga umarnin shugaban ƙasa ga jagororin tsaro na su tare a Jihar Borno, Gwamnatin Tarayya tana ƙara ƙarfafa wa dakarun tsaro da kayan yaƙi domin yaƙar ta'addanci a sassan ƙasar da ke cigaba da addabar al'umma. Shettima ya bayyana haka ne a jiya Laraba a Maiduguri yayin wata ziyarar duba marasa lafiyar da harin bom ya rutsa da…
Read More

Sarki Charles ya marabci Tinubu da Oluremi cikin karamci a Birtaniya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu kyakkyawar tarba daga Sarki Charles na III a yau Laraba yayin wata ziyarar ƙarfafa alaƙar Nijeriya da Birtaniya. Duk da cewa shugaban ƙasar ya ziyarci Birtaniya a lokuta da dama tun bayan hawansa mulki, wannan ita ce ziyarar aiki ta farko tsakanin ƙasashen cikin kusan shekaru 37. Tinubu ya samu rakiyar matarsa, Oluremi Tinubu da sauran muƙarrabansa na Gwamnatin Tarayya. An karrama su da sarawa ta bindiga da ake kira da'42-gun salute' daga sojojin sarki na 'Royal Horse Artillery'. Gabanin haka Yarima William da Gimbiya Catherine sun gana…
Read More

Yanzu-yanzu: Ba a ga wata Saudiyya ba, za a yi sallah ranar Juma’a

Hukumomi a ƙasar Saudi Arabia sun sanar da cewa ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a ko’ina cikin ƙasar a wannan rana, lamarin da ya sa aka yanke shawarar cika watan Ramadan kwana 30. Sanarwar ta nuna cewa sakamakon rashin ganin watan, za a ci gaba da azumi gobe domin cika kwanaki 30 na watan Ramadan, kafin a gudanar da bikin Ƙaramar Sallah a ranar Juma’a, 20 ga Maris, 2026. Kwamitocin duban wata da cibiyoyin lura da taurari a faɗin ƙasar sun gudanar da bincike a wurare daban-daban, amma duk da haka ba a samu tabbacin ganin jinjirin watan…
Read More

Kofin Duniya na 2026: NFF ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin FIFA na cancantar da DR Kongo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar kula da Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa (NFF) ta fara shirye-shiryen ɗaukaka ƙara akan hukuncin FIFA na yin watsi da ƙorafinta akan Dimukraɗiyyar Jamhuriyar Kongo bisa rashin cancantar wasu 'yan wasa da ƙasar ta yi amfani da su a wasanta da Nijeriya na neman gurbi a gasar Kofin Duniya na 2026, wanda aka gudanar a ranar 16 ga Nuwamban 2025 a Moroko. Babban Sakataren NFF Dakta Muhammad Sanusi ya bayyana cewa, ba su gamsu da hukuncin hukumar ƙwallon ƙafar ta duniya ba, don haka suka fara yunƙurin ɗaukaka ƙara a kai. A cikin ƙorafin,…
Read More

Eid-Al-Fitr: Sarkin Musulmi ya umarci a fara duba jinjirin watan Shawwal daga Laraba

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar na III, ya yi kira ga al’ummar Musulmi a fadin Nijeriya da su fara neman jinjirin watan Shawwal, wanda ke nuna ƙarshen azumin watan Ramadana da kuma shigowar bikin Sallah ƙarama, wato Eid-el-Fitr. Sanarwar ta fito ne ta hannun Sambo Wali Junaidu a madadin Majalisar Masarautar Sarkin da ke Sakkwato. A cewar sanarwar, ranar Laraba 18 ga Maris, 2026, wadda ta yi daidai da 29 ga Ramadan 1447AH ita ce aka ware domin duban jinjirin watan. Sarkin Musulmin, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Ƙolin Harkokin Addinin Musulunci, ya…
Read More

Babban jami’in yaƙi da ta’addanci na Trump ya yi murabus kan yaƙar Iran

Daraktan cibiyar yaƙi da ta'addanci na ƙasar Amurka ya sanar da ajiye aiki a shafinsa na soshiyal midiya, inda ya ce "tunaninsa bai amince masa ya goyi bayan yaƙin da ake yi kan Iran ba". Majalisar dattawan Amurka dai ta tabbatar da Joe Kent a matsayin mutumin da Trump ya zaɓo domin cike gurbin a watan Yulin bara. Da yake yi wa Trump bayani a wasiƙar ajiye aikin, Kent ya ce "Iran ba ta barazana ga ƙasarmu, kuma a bayyane take cewa mu ne muka fara wannan yaƙi saboda matsin lamba daga Isra'ila da masu neman mata gindin zama masu…
Read More

Tinubu ya umarci jagororin tsaro su koma Maiduguri bayan munanan hare-haren ƙunar baƙin-wake

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya umarci jagororin rundunonin tsaro da su gaggauta komawa Maiduguri bayan wasu munanan hare-haren ƙunar baƙin-wake da suka auku a birnin na Jihar Borno a jiya Litinin. Tinubu ya ɗauki matakin ne da nufin ƙarfafa ayyukan tsaro a shiyyar da ke fama matsalar taɓarɓarewar harkar. A wata takarda ga manema labarai, Shugaban ƙasar ya bayyana kaɗuwarsa game da rasa rayukan da aka yi da kuma jikkata da wasu suka samu a sanadiyyar faruwar tashin ababen fashewar, yana mai jajenta wa iyalai da abokan arziƙi game da rashin da aka yi musu.…
Read More

Ƙungiyoyin matasa sun ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya a taron buɗe baki na Musulmi da Kiristoci a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar 'Youth Development Initiatives', ta jagoranci taron buɗe bakin azumin Ramadana da Lent na Musulmi da Kiristoci, inda ta jaddada ƙoƙarinta na cigaba da kira ga mutuntawa tsakanin addinai, zaman lafiya da wayar da kan masu zaɓe acikin 'yan Nijeriya. Shugaban ƙungiyar, Dakta Ameer Lukman Haruna ne ya shirya taron, wanda ya ƙunshi shugabannin al'umma, jagororin jam'iyyun siyasa na matasa da wakilan gidajen jarida a wani yanayi na mutunta juna, inda aka kuma aka yaɗa saƙonnin samar da haɗin kai a tsakanin mabanbanta addinai da harkokin siyasa. Da yake jawabi a taron, Dakta Lukman…
Read More

Isra’ila ta yi iƙirarin halaka Shugaban rundunar tsaron Iran a yaƙin Gabas ta tsakiya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ministan Tsaron Isra’ila, Isreal Katz, ya bayyana cewa Ali Larijani, Shugaban dakarun tsaron Iran, an hallaka shi a wani farmaki da aka kai da daddare. A cewar wata sanarwa daga ma’aikatar tsaron Isra’ila, Katz ya ƙara da cewa Gholamreza Soleimani, shugaban rundunar Basij, shima an kashe shi a wannan aiki guda. Rundunar Basij, wadda ɗaya ce daga cikin muhimman sassan Islamic Revolutionary Guard Corps IRGC, tana da babban rawa wajen tsaron cikin gida na Iran. Hakan na zuwa ne ƙasa da makonni uku da aka fara gwabza yaƙi tsakanin Iran da Amurka da Isra’ila…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: An rantsar da Soludo a matsayin gwamnan Anambara karo na biyu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An sake rantsar da Farfesa Chukwuma Soludo a matsayin gwamnan Jihar Anambara a karo na biyu a hukumance. Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima tare da tsoffin shugabannin ƙasa Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan, sun isa filin jirgin sama na Chinua Achebe domin halartar bikin rantsar da gwamnan. Rahotanni sun tabbatar da cewa, manyan baƙin sun sauka lafiya, inda gwamnatin jihar ta shirya tarba ta musamman domin wannan muhimmin biki. An gudanar da bikin ne a filin Alex Ekwueme Square, wanda aka gyara kwanan nan. Manyan mutane daga sassa daban daban na ƙasar nan sun…
Read More