Babaji

5689 Posts

UCL: Madrid ta saka manyan ‘yan wasanta cikin tawagar da za ta gwabza da Man City duk da babbar nasara a wasan farko

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta tabbatar da tawagar 'yan wasanta da za su fafata a Manchester City a wasa na biyu na zangon 'yan 16 a gasar Zakarun Nahiyar Turai, UEFA Champions League. Za a buga wasan ne a filin wasa na Etihad da ke birnin Manchester a ƙasar Ingila a gobe Laraba. Babban labari a wasan shi ne zaƙakuran 'yan Madrid da ba su samun buga wasan farko ba a yanzu sun dawo cikin tawagar, waɗanda suka haɗa da Kylian Mbappe, Jude Bellingham da kuma Alvaro Carreras. A wasan farko da…
Read More

‘Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 23 yayin da 108 suka jikkata a harin boma-boman Maiduguri

Rundunar ‘yan sanda a Jihar Borno, ta tabbatar da cewa mutane 23 sun mutu, yayin da wasu 108 suka jikkata sakamakon wasu fashe-fashe da suka girgiza Maiduguri a yammacin ranar Litinin, abin da hukumomi suka bayyana a matsayin hare-haren ƙunar baƙin-waken da aka tsara a tare. Al'amarin ya auku ne da misalin ƙarfe 7:24, inda aka kai hare-haren a wurare masu cinkoson da muhimmanci a cikin birnin, ciki har da Kasuwar Litinin ta Maiduguri, kofar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, da gadar sama ta Post Office. A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, ASP Nahum…
Read More

Sojoji sun kama ɗan bindigar TikTok Sule Yalo bayan karɓar fansa

Jami'an Rundunar Sojoji sun yi nasarar kama wani matashi da ake zargi da alaka da ‘yan bindiga mai suna Sule Yalo, wanda aka ce yana amfani da shafin TikTok da sunan @suleyellow6, bayan zargin cewa yana karɓar kuɗin fansa daga iyalan waɗanda aka sace tare da tallata ayyukan ‘yan bindiga a kafafen sada zumunta. Rahotanni sun bayyana cewa an kama Sule Yellow ne bayan jami’an tsaro sun fara zargin sa sakamakon yadda yake bayyana a shafukan sada zumunta da kuma alakar da ake zargin yana da ita da wasu masu aikata laifuka. An kuma ce a ranar 4 ga watan…
Read More

Borno: Boko Haram ta kai sabon farmaki a sansanin sojoji

Mayakan ƙungiyar Boko Haram sun sake kai wani hari a sansanin sojojin Nijeriya dake jihar Borno, lamarin da ya ƙara nuna yadda hare-haren ‘yan ta’adda ke ƙaruwa a yankin Arewa maso Gabas na ƙasar. Rahotanni sun ce maharan sun kai harin ne a wani sansanin soja da ke Ajilari, wani yanki da ke kusa da birnin Maiduguri, babban birnin jihar. Harin ya faru ne da sanyin safiyar Litinin inda aka ce an ji ƙarar harbe-harbe da fashe-fashe a yankin. Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa mayakan sun farmaki sansanin sojojin ne da makamai masu karfi, lamarin da ya janyo arangama…
Read More

An sake zaɓar Laporta a matsayin shugaban Barcelona zuwa 2031

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rahotanni sun bayyana cewa an sake zaɓen Joan Laporta a matsayin shugaban FC Barcelona bayan ya samu gagarumar nasara a zaɓen da aka gudanar a ƙarshen makon da ya gabata. Laporta ya samu ƙuri’u 32,934 wanda ya kai kashi 68.18, inda ya doke babban abokin hamayyarsa Víctor Font mai ƙuri’u 14,385, wato kaso 28.78. Hasashen farko daga kafafen yada labarai na Cataloniya sun bayyana cewa da fari alamu sun nuna Laporta ne zai lashe zaɓen. Dubban mambobin ƙungiyar, waɗanda ake kira socios, sun fito domin kaɗa ƙuri’arsu, lamarin da ya ba Laporta damar sake…
Read More

Tinubu ya rantsar da Taiwo Oyedele a matsayin ƙaramin ministan kuɗi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da Taiwo Oyedele a matsayin ƙaramin ministan kuɗi. Shugaban ya rantsar da shi ne a jiya Litinin a wani taƙaitaccen bikin rantsuwar da ya gudana a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. A makon da ya gabata ne Majalisar Dattawa ta tabbatar da Oyedele a matsayin ministan bayan Tinubu ya naɗa shi. Haka kuma, a ranar 3 ga Maris ne Tinubu ya miƙa sunan Oyedele ga majalisar a wata takarda da ya aike wa Shugabanta, Sanata Godswill Akpabio inda ya buƙaci a tabbatar da shi a muƙamin kamar yadda…
Read More

Tinubu ya umarci a raba shinkafa ga Musulmi da Kiristoci yayin Ramadana da Lent

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya umarci Jakadun Shriin Sabunta Fata (Renewed Hope Ambassadors) da su raba shinkafa ga ‘yan Nijeriya a duk faɗin ƙasar domin tallafa wa masu azumin Ramadana da kuma Kiristoci da ke yin na Lent. Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, wanda shi ne Darakta Janar na shirin ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 14 ga Maris, 2026. A cewar Uzodimma, shirin rabon shinkafar na nufin ƙarfafa haɗin kan ƙasa da kuma nuna tausayi ga ‘yan ƙasa a wannan lokaci mai muhimmanci na ibada ga Musulmi…
Read More

Mutane da dama sun rasu yayin da boma-bomai suka fashe a Maiduguri

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Al'ummar Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno, sun shiga firgici a jiya Litinin sakamakon fashewar boma-bomai a wurare mabanbanta a birnin, lamarin da ya yu ajalin mutane da dama. Ana zargin 'yan ta'addar Boko Haram ne suka dasa ababen fashewar, waɗanda suak tarwatse jim-kaɗan bayan shan ruwa. Shaidun gani da ido sun ce tashe-tashen boma-boman sun jefa tsoron acikin al'ummar yankunan da ke kusa da waejn da abin ya faru, wanda ya sa da dama suka riƙa ƙaurace wa wuraren da ake fargabar aukuwar wani hari. Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, Nahum Daso Kenneth…
Read More

Birtaniya ta fitar da tsarin shirye-shiryen ziyarar Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Birtaniya ta fitar da jadawalin ziyarar Shugaba Bola Tinubu, wadda za a gudanar daga ranar 17 zuwa 19 ga watan Maris, 2026. A cewar jadawalin, za a karɓi shugaban ne a Windsor Castle, inda zai halarci tarurrukan tattaunawa tsakanin kasashen biyu, bukukuwan girmamawa, da kuma ganawa da ‘yan Najeriya mazauna Birtaniya. An tsara fara shirye-shiryen ziyarar a ranar 17 ga Maris, inda jami’an tsaro za su gudanar da bincike, rufe wasu hanyoyi, da kuma atisayen jerin gwanon tarba kafin isowar shugaban. Tinubu zai isa Birtaniya a hukumance a ranar 18 ga Maris, inda…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta fallasa shirin tozarta Tinubu yayin ziyarar Birtaniya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta ce ta gano wani shiri da wasu kamfanonin haƙar ma’adinai na ƙasashen waje ke yi domin ɓata wa Shugaba Bola Tinubu suna a yayin ziyararsa a Birtaniya. A cewar Ma'aikatar Ci-gaban Ma'adinai da Ƙarafuna ta Ƙasa, wani kamfani mai suna Jupiter Ltd na shirin kaddamar da manufa ta yaɗa jita-jita da ɗaukar nauyin zanga-zanga domin kunyata shugaban ƙasar a lokacin ziyarar. Mataimakin Ministan Ma’adanai kan harkokin yaɗa labarai, Segun Tomori, ya ce kamfanin na shirin ɗaukar nauyin kamfen a kafafen yaɗa labarai domin sukar gwamnatin tarayya kan matakan da take ɗauka…
Read More