12
Mar
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja 'Yan bindiga sun sako mutane 16 da suka yi garkuwa da su a lokacin hidimar bikin aure a Ƙaramar Hukumar Tafawa Ɓalewa ta Jihar Bauchi bayan an biya su fansar Naira miliyan 25. Daga cikin waɗanda abin ya shafa akwai wata amarya da 'yan tawagarta, waɗanda suka shafe kwanaki 57 a komar 'yan bindigar kana aka sako su bayan biyan kuɗin fansar da ƙyar. A ranar 10 ga watan Junairu aka yi awon-gaba da shi a bikin, wanda ya ƙunshi iyalan wani Malam Abubakar Santuraki Ubandoman Lim na garin Gwammadaji da ke Gundumar Dull…
