Babaji

5689 Posts

DSS ta kama ɗan TikTok, Waspapping a Kaduna kan yaƙin Amurka/Isra’ila da Iran

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, ta kama wani mai sharhi a kafafen sada zumunta mai suna Sani Waspapping, wanda ake kira “Sarki” a dandalin X. Rahotanni sun ce an kama shi ne a yammacin ranar Juma’a a kusa da NEPA Roundabout a birnin Kaduna. Saidai ba a bayyana takamaiman zargin da ake yi masa ba. Wasu abokansa sun ce an kama shi ne saboda ra’ayoyin da ya bayyana kan yaƙin tsakanin Amurka da Isra’ila a gefe guda da kuma Iran a ɗaya ɓangaren. Rahoton ya ce an kama shi tare da wani abokinsa,…
Read More

Mu ne za mu yanke hukuncin lokacin da yaƙin zai ƙare – Martanin Iran kan kalaman Trump na yaƙinsu ya kusa ƙarewa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar juyin juya halin ƙasar Iran ta yi watsi da kalaman Shugaba Donald Trump na cewa yaƙin da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar akan Iran ya kusa ƙarewa, yayin mayar da martani akan furucin shugaban Amurkan. Trump ya bayyana a wani taro a Florida cewa Amurka ta samu gagarumar nasara a yaƙin, kuma akwai yiwuwar kawo ƙarshensa nan kusa. Shugaban Amurka ya ce Iran na shirin kai hari kan Amurka kuma tana ƙoƙarin farfado da shirinta na Nukiliya. A kan yiwuwar kai hari kan sabon jagoran addinin Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei, Trump ya ce…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta san suna da wajen da kowane ɗan ta’adda yake, inji Sheikh Gumi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sanannen Malamin addinin Musulunci a Nijeriya, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta san sunayen dukkan ‘yan ta’addan da ke addabar ƙasar tare da wuraren da suke ɓoye kansu. Gumi ya ce bayanan da hukumomin tsaro ke da su sun isa su gano kowane dan ta’adda, domin a cewarsa, "sun san su da suna, sun san inda suke zaune, tare da wuraren da suke gudanar da ayyukansu." Ya bayyana cewa abin da ake bukata yanzu shi ne daukar matakai masu ƙarfi da kuma amfani da dabaru na musamman domin kawo ƙarshen matsalar…
Read More

Farashin mai ya karye a duniya bayan Trump ya ce yaƙin Iran ya ƙare

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Farashin mai ya sauka cikin sauri bayan ya yi tashi gwauron zabo duniya suka samu tashin gwauron zabo yayin da Shugaba Donald Trump na Amurka ya bayyana cewa yaƙin da ƙasarsa ke yi tare da Isra’ila akan Iran ka iya ƙarewa da wuri fiye da yadda aka tsammani. Trump ya ce wannan ci-gaba na iya rage fargabar da ke damun kasuwanni a duniya, inda hakan ya sa masu saka jari suka fara mayar da hankali kan damar samun riba a kasuwannin hannun jari. Wannan yanayi ya kawo kwanciyar hankali a wasu ɓangarori na tattalin…
Read More

Matatar Ɗangote ta rage farashin fetur da dizal

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Matatar Mai ta Ɗangote ta rage farashin fetur da N100, inda ya sauka daga N1,175 zuwa N1,075 akan kowace lita. Haka kuma farashin dizal ya ragu da N190, daga N1,620 zuwa N1,430 kan kowace lita. Hakan na zuwa ne bayan saukar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya, wanda da fari ya haura sakamakon rikicin yankin gabas ta tsakiya. Masana na ganin matakin na iya kawo ɗan sauƙi ga ‘yan kasuwa, yayin da ake sa ran hakan zai iya sa farashin mai a gidajen mai ya ragu a faɗin Nijeriya. Matatar ta nuna cewa farashin…
Read More

Za su farmake mu cikin mako guda, inji Trump bayan gano ƙarfin makaman Iran ya wuce yadda yake tunani

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce Iran tana da makamai masu linzami sama da yadda ake tunani da fari, wanda hakan ya sa take shirin kai wa Amurka hari. Trump ya bayyana haka ne a jiya Litinin yayin jawabi ga 'yan majalisa na jam'iyyarsa ta Republican a taron shekara-shekara na nazarin tsare-tsaren da aka yi a Florida. A cewarsa, ƙasar za ta iya kai musu hari cikin mako ɗaya duba da shirin da suka yi wa yaƙin. Hakan na zuwa ne jim-kaɗan bayan jawabin Shugaban na Amurka cewa hare-haren soji da take kai…
Read More

Kwara: Ƙungiyar Shiya Development ta yi ƙorafin salon naɗin sarkin Masarautar Okuta

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Shiya Development a Jihar Kwara, ta yi ƙorafin salon naɗin sarkin Masarautar Okuta da ke Ƙaramar Hukumar Baruten ga Hukumar kare 'yancin ɗan-adam (NHRC). A ranar 4 ga watan Nuwamba, 2024 ne aka samar da hanyoyin zaɓen sarkin gargajiya a yankin sakamakon samun gurbin hakan da aka yi. Saidai al'amarin ya samu tsaiko sakamakon rashin kiyaye ƙa'idojin da aka gindaya daga mambobin kwamitin zaɓen. A wata takarda da Shugaban ƙungiyar, Yakubu Kio ya fitar, Shiya Development Association ta bayyana cewa al'ummar Okuta sun koka ganin yadda ɗan takarar da suka amince da shi…
Read More

Ramadana: MOPPAN ta jinjina wa ‘yan Kannywood bisa tallafa wa al’umma

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar masu Shirya finafinai ta Ƙasa (MOPPAN) ta yaba wa wasu daga cikin jaruman finafinan bisa hoɓɓasa da suak yi wajen raba wa al'umma tallafin kayan abinci domin sauƙaƙa musu halin matsin rayuwa yakin azumin watan Ramadana. A wata takarda da ta fitar a ranar Litinin ta hannun Sakataren, Dakta Mohammed Ibrahim Gumel, MOPPAN ta ce jaruman sun yi abin da ake buƙata musamman ganin yadda malamai suke faɗakarwa akan falalar taimakon marasa galihu. A cewar sanarwar, ababen da aka raba wa mabuƙatan sun haɗa da shinkafa, taliya, ababen hawa, tsabar kuɗi da dai…
Read More

Amurka ta yi gargaɗin aukuwar munanan hare-hare akan ofisoshinta da makarantu a Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ofishin Jakadancin Amurka a Nijeriya ya fitar da saƙon ankararwa ga al'umma, inda ya yi gargaɗin yiwuwar aukuwar munanan hare-hare daga 'yan ta'adda waɗanda ke harin ofisoshin Amurka da makaratu masu haɗaka da ƙasar a Nijeriya. A wani rubutu da ya fitar a Abuja, ofishin jakadancin ya shawarci 'yan Amurka da ke Nijeriya da su kula yayin kai ziyara a wuraren harkokin jakadancin Amurka da cibiyoyi masu alaƙa da ita. Musamman saƙon ya fi mayar da hankali akan ofisoshin jakadancin Abuja da Legas, inda ya yi kira a gare su da kasance masu sanya…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: An bada rahoton halaka Fraministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Litinin kafar yaɗa labarai ta Tasnim a ƙasar Iran ta yi zargin cewa akwai yiwuwar Fraministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya rasu ko ya jikkata a yayin da yaƙi tsakanin ƙasashen biyu ya yi ƙamari. A wani rubutu da ta wallafa wanda ya karaɗe kafafen sadarwa, kafar ta yi ikirarin ne sakamakon rashin ganin sababbin hotuna ko bidiyonsa. An gano cewa bidiyonsa na ƙarshe da aka wallafa a sahihin shafinsa ya kai kusan makonni uku, yayin da hotunan ƙarshe kuwa sun kai tsawon kwanaki huɗu. Tun daga lokacin saidai a ga wasu rubuce-rubuce…
Read More