09
Mar
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Kula da Harkokin Ƙwallon Ƙafa ta Duniya FIFA, ta ayyana ranar 30 ga watan Mayu a matsayin lokacin da za ta rufe amsar jerin sunayen 'yan wasan ƙasashen da za su fafata a gasar Kofin Duniya na 2026. A cewar umarnin, kowace ƙasa wajibci ne ta miƙa tawagar sunayen 'yan wasa guda 25 domin fafatawa a gasar, wanda haka aka yi a lokacin gasar ta 2022. Wannan mataki ya bai wa tawagogin ƙasashen damar ɗaukar adadin 'yan wasa masu yawa domin magance dukkan wasu matsaloli da ka iya shafar su kamar na jin…
