Babaji

5689 Posts

Kotu ta amince da buƙatar ICPC ta bincike na’urorin da ta samo a gidan El-Rufa’i

Babbar Kotun Tarayya ta ba Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC izinin shiga da binciken bayanai daga wasu na’urorin lantarki da aka kwato daga gidan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai. Mai shari’a Joyce Abdulmalik ce ta bayar da umarnin a ranar Alhamis bayan ta amince da bukatar da ICPC ta gabatar ta hannun lauyanta, Dr. Osuobeni Akponimisingha. ICPC ta bayyana cewa tana bukatar duba na’urorin ne domin gudanar da binciken fasaha (forensic examination) da kuma fitar da bayanai domin ci gaba da binciken da take yi kan tsohon gwamnan. Na’urorin da ake son bincika sun hada…
Read More

An samu ƙarin matsi ga ‘yan Nijeriya yayin da Ɗangote ya sake ƙara farashin fetur sa’o’i bayan ragewa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Farashin fetur ya sake hawa zuwa N1,175 a matatar Dangote sa'o'i bayan sanar da ragewa. Matatar ta sake ɗaga farashin fetur zuwa N1,175 akan kowace lita. A baya dai matatar ta rage farashin fetur da N100, wanda farashin ya sauka zuwa N1,075 akan lita a ranar 10 ga Maris, 2026, wato daga N1,175. Bayan sabon karin farashin, masu sayar da mai a manyan rumbunan ajiya (depots) sun dakatar da sayar da fetur na ɗan lokaci domin tantance sabon tsarin farashin. Wannan al'amari ya sake jefa 'yan Nijeriya cikin matsi musamman bisa la'akari da halin…
Read More

Wasan Madrid da Man City bai ƙare ba, inji Doku gabanin karawa ta biyu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗan wasan gaba na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City Jeremy Doku ya ce har yanzu City tana da amannar cewa za ta iya farfaɗowa dafa lallasar da Real Madrid ta yi mata a karawar farko da suak yi a tsakaninsu a gasar Zakaran Nahiyar Turai, wato Champions League. A cewarsa, akwai buƙatar magoya bayan City su sanya matsi ga 'yan wasan Madrid, yana mai cewa a ƙwallon ƙafa komai na iya faruwa don haka suke ganin za su iya yin nasara a wasa na biyu da za a fafata a filin Etihad. Hakan…
Read More

ADC ta wa PDP zarra a Majalisar Dattawa yayin da ƙarin ‘yan mambobi suka sauya sheƙa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Aƙalla sanatoci guda tara daga jam’iyyu uku sun sanar da Majalisar Dattawa cewa sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar adawa, ADC. Sanatocin da suka fice jam'iyyar LP sun haɗa da Victor Umeh, Tony Nwoye da Ireti Kingibe. Sauran biyar kuwa, sun fice ne daga PDP waɗanda sune: Aminu Waziri Tambuwal, Binos Yaroe, Lawal Adamu Usman, Mohammed Ogoshi Onawo da Augustine Akobundu. Haka kuma Enyinnaya Abaribe daga APGA shi ma ya koma ADC, sai dai Majalisar Dattawa ta ba shi wa’adin mako guda ya sake nazarin matakin, tana mai cewa hujjar da ya bayar ta ficewa…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi An tabbatar da mutuwar sojojin Amurka huɗu bayan jirginta ya yi hatsari a Iraƙi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Huɗu daga cikin sojojin Amurka shida sun rasu a lokacin da jirgin ƙasar ya yi hatsari a yankin Yammacin Iraƙi, kamar yadda Cibiyar Tsaron Amurka (Centcom) ta bayyana. Centcom ta ce ana cigaba da aikin ceto bayan ƙwacewar jirgin mai ƙirar KC-135, duk da cewa da farin ta ce bai kama da wuta ba a lokacin faruwa al'amarin. Jirgin yana cikin waɗanda ke taimaka wa masu kai farmaki a yaƙin da ake cigaba gwabzawa tsakanin Amurka da Iran, kuma yana ɗaya daga cikin jirage biyu da iftila'in ya afka wa. A cewar Centcom, al'amarin…
Read More

Abin a yaba: Likitocin Nijeriya sun yi nasarar cire ƙarin ƙwaƙwalwa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A wani yanayi na sauyin rayuwa na dare ɗaya a watan Agustan 2024, Babangida Ibrahim ya tunatar da yadda ya rasa kansa a lokaci guda wanda ya haifar da rikicewa sama da raɗaɗil, lamarin da ya janyo tsaiko ga kwanciyar hankalinsa a wannan lokaci. Blueprint ta ruwaito cewa, Ibrahim ya kwanta cikin ƙoshin lafiya bisa rashin sanin yana dab da shiga halin buƙatar gaggawa akan cutar ƙwaƙwalwa da ke neman jarraba tunaninsa akan rashin lafiya, imani da kuma sauyin ci-gaba a fannin harkar lafiya a Nijeriya. A yayin da yake barci ne sai jikinsa…
Read More

Kotu ta haramta wa Aiyedatiwa neman wani wa’adin gwamna a Ondo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Akure, Babban Birnin Jihar Ondo, ta yanke hukuncin cewa Gwamna Lucky Aiyedatiwa bai da damar sake tsayawa takarar wani wa'adin mulki a kujerar. Da yake gabatar da hukuncin a ranar Alhamis, Mai Shari'a Toyin Bolaji Adegoke ya bayyana cewa kundin tsarin dokokin Nijeriya na 1999 (da aka yi wa kwaskwarima) bai ba wa zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa, gwamna ko mataimakin gwamna damar cigaba da riƙe muƙamin ba na tsawon sama da shekaru takwas. Kotun ta yi wannan hukunci ne bayan gabatar da wani ƙorafi…
Read More

Shugaban PDP a Zamfara ya koma APC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara, Dakta Jamil Jibo Magayaki, ya sanar da ficewar sa daga jam’iyyar tare da koma wa mai mulki, wato APC. Magayaki ya bayyana sauya sheƙar tasa ne kwanaki kaɗan da Gwamnan jihar, Dauda Lawal ya koma APC. A wata sanarwa da ya wallafa a shafukan sada zumunta, tsohon shugaban PDP na Zamfara ya ce ya ɗauki wannan mataki ne bisa la’akari da halin siyasar da ake ciki a jihar. Ya ce, "Ni, Dakta Jamil Jibo Magayaki, shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Zamfara, ina sanar da komawata a hukumance zuwa…
Read More

Shi’ah ta magantu kan zargin farmakar Amurkawa, ta sanya ranar gangami a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) da aka sani da Shi'ah ta ƙaryata zarge-zargen cewa ta shirya kai farmaki akan Amurkawa ko cibiyoyinsu da ke Nijeriya, tana mai cewa ayyukanta suna nan cikin lumana kuma a dokance. Haka kuma, ta ce ta zaɓi Juma'a, a matsayin ranar Quds da za ta yi gangaminta da kuma jimamin mutuwar jagoran addinin ƙasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei. Hakan na zuwa ne bayan da ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya ya fitar da saƙon ankararwa ga Amurkawa kan yiwuwar 'yan ta'adda ka iya kai hari akan ofisoshin Amurka na…
Read More

Gwamnatin Tarayya na shirin faɗaɗa amfani da gas da motocin lantarki don rage tsadar sufuri — PCNGi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban Shirin Bunƙasa Amfani da Iskar Gas na Shugaban Ƙasa (PCNGi), Isma'eel Ahmad, ya ce gwamnati na ƙara ƙaimi wajen faɗaɗa amfani da gas da motoci masu amfani da lantarki domin rage tsadar sufuri a Najeriya. Ismaeel ya bayyana haka ne bayan ganawarsa da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, inda suka tattauna kan hauhawar farashin fetur da rikicin Gabas ta Tsakiya ya haddasa, da kuma hanyoyin da shirin PiCNG da motocin lantarki (EV) za su taimaka wajen magance matsalar. Ya ce, ya gabatar wa shugaban ƙasar da shirin da hukumar ke da shi na…
Read More