Babaji

5689 Posts

Iran ta kai wa ofishin jakadancin Amurka hari a Bagdaza

Yayin da ake cigaba da gwabzawa a yaƙin Gabas ta tsakiya, wani hari ya auku a harabar ofishin jakadancin Amurka da ke Bagadaza, babban birnin ƙasar Iraƙi. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wasu majiyoyi na cewa an ga hayaƙi na tashi daga ginin jakadancin bayan harin. Haka kuma, Rahoton Associated Press ya ce makami mai linzami ne ya faɗa kan filin sauka da tashin jirage masu saukar ungulu a harabar ofishin. Sai dai Agence France-Presse ta ruwaito cewa jirgi marar matuƙi ne ya kai harin. Rahotanni sun ce harin ya faru ne jim kaɗan bayan kashe wasu mayaƙa…
Read More

Jami’in Cibil Defense ya rasa ransa yayin rabon tallafin Ramadana a Kano

Rahotanni sun bayyana cewa wani jami’in Tsaro na Civil Defence ya rasa ransa yayin da yake ƙoƙarin kare jama’a a lokacin da wasu ‘yan daba suka kai hari a wani taron rabon tallafi. Lamarin ya faru ne a lokacin da Hon Alhassan Ado Doguwa, ke ƙaddamar da rabon tallafin shinkafa da kuma kudade kimanin Naira miliyan 20 ga al’umma a Jihar Kano. A yayin gudanar da taron ne wasu matasa da ake zargi ‘yan daba ne suka kai farmaki tare da yunkurin sace kudaden. Hadimin Dan majalisar kan yada labarai Auwal Ali Sufi yace maharan sun yi nasarar kwashe kimanin…
Read More

Majalisar Dattawa ta tabbatar da Ɗakingari da Isma’il Yusuf a matsayin jakada da shugaban NAHCON

Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin Ambasada Ismail Abba Yusuf a matsayin Shugaban Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON). Hakan ya biyo bayan rahoton kwamitin harkokin waje na majalisar dattawa, wanda Sanata Abubakar Sani Bello (APC, Niger North) ke jagoranta, bayan sun yi masa tantancewa. A zaman majalisar da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya jagoranta, majalisar ta kuma amince da naɗin Alhaji Saidu Usman Dakingari a matsayin jakadan Najeriya wanda ba ma’aikacin diflomasiyya na dindindin ba (Non-Career Ambassador). Kazalika, majalisar ta tabbatar da naɗin Rear Admiral Jamila Abubakar Sadiq (mai ritaya) a matsayin Kwamishinan Zaɓe na ƙasa a Hukumar Zaɓe…
Read More

Ramadana: Gwamnan Sokoto ya amince da biyan albashin Maris gabanin Ƙaramar Sallah

Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu Sokoto, ya amince da fara biyan albashin watan Maris tun daga ranar Juma’a 13 ga watan Maris, domin bai wa ma’aikatan gwamnati damar gudanar da shagulgulan Sallah cikin sauƙi.‎‎Sanarwar ta fito ne ta bakin Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gidan Gwamnatin Jihar, Malam Abubakar Bawa.‎‎A cewar sanarwar, biyan albashin zai shafi dukkan ma’aikatan gwamnatin jiha, ma’aikatan ƙananan hukumomi, da kuma masu karɓar fansho a faɗin jihar.‎Gwamna Ahmed Aliyu, wanda a halin yanzu yake ƙasar Saudi Arabia domin gudanar da ibadar Umrah, ya buƙaci ma’aikatan gwamnati su cigaba da nuna ƙwazo, gaskiya da…
Read More

CBN ya umarci bankuna su saka takunkumi ga masu asusun da suka saɓa sharuɗɗan karɓar bashi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya umarci bankuna su hana bayar da sabon bashi ga kwastomomin da rancensu ya zama wanda aka gaza musamman manyan masu bashi. Sanarwar da Daraktan Kula da Bankuna, Olubukola Akinwunmi ya sanya wa hannu ta ce duk wanda aka saka sunansa a tsarin Credit Risk Management System (CRMS) ko bayanan cibiyoyin bashi, to ba zai samu sabon lamuni ba. Haka kuma, za a sanya masa takunkumi na wasu ayyukan banki da za su bayar da damar samun wani ƙarin bashi. Babban bankin ya kuma ce matakin ya shafi manyan masu…
Read More

ISWAP ta fitar da hoton ɗan ƙunar baƙin-waken da ya farmaki sansanin sojoji a dajin Sambisa

Kungiyar Islamic State West Africa Province (ISWAP) ta fitar da hoton wanda ta ce shi ne dan kunar bakin wake mai suna Abu Hafsah al-Ansari, wanda ya kai hari kan sansanin wucin gadi na rundunar sojin Najeriya 21st Special Armored Brigade a cikin Sambisa Forest a makon da ya gabata. A cewar kungiyar, harin ya kai hari ne kan sansanin sojoji na wucin gadi, inda ta yi ikirarin cewa adadin wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata a cikin sojojin Najeriya ya kai mutum 30. Sai dai a irin wadannan lokuta, rahotannin da kungiyoyin ‘yan ta’adda ke fitarwa kan yawan…
Read More

Yanzu-yanzu: Tinubu ya kafa kwamitin ko ta-kwana a fannin fetur

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya amince da kafa wani kwamitin musamman mai suna 'Presidential Petroleum Reform & Value Optimisation Taskforce' domin tsara sabon mataki na tsarin gyare-gyaren harkokin man fetur a Nijeriya. A sanarwar Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya fitar, an bayyana cewa tsohon shugaban banki kuma wanda ya kafa Guaranty Trust Bank, Fola Adeola shi ne zai jagoranci kwamitin a matsayin shugaba. Wannan ya nuna shi zai riƙa kula da tafiyar da ayyukan kwamitin tare da tabbatar da an kammala aikinsa cikin lokaci. Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Ademola Adeyemi-Bero, Osagie Okunbor,…
Read More

Yanzu-yanzu: Amurka ta sanya ladar Dala miliyan 10 ga wanda ya fallasa inda sabon jagoran addinin Iran yake

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da cewa za ta bayar da ladan Dala miliyan 10 ga duk wanda ya bayar da sahihan bayanai akan inda sabon jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei, da Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, Ali Larijani suke. Amurka ta ce an sanya ladan ne saboda zargin da take yi cewa shugabannin biyu na da alaƙa da ayyukan rundunar juyin juya hali ta Iran, IRGC. Rahotanni sun bayyana cewa duk wanda ya bayar da bayanai masu amfani zai iya samun ladar kuɗi tare da kariyar tsaro da sauya masa wurin…
Read More

Kano, Katsina, Adamawa da wasu jihohi takwas ne suka fi samun haɗarin kamuwa da sanƙarau

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa (NiMet), ta yi gargaɗin cewa jihohi guda 11 na arewacin Nijeriya na cikin haɗarin ɓarkewar cutar sanƙarau yayin da bushewar kakar rani ke ƙara hauhawa. NiMet ta lissafo jihohin Sakkwato, Zamfara, Kebbi, Katsina, Kano, Jigawa, Adamawa, Gombe, Bauchi, Yobe da Borno a matsayin yankunan da ke da haɗarin kamuwa da cutar, wadda kira da Cerebrospinal Meningitis. A cewar hukumar, sankarƙau cuta ce da kwayar Neisseria meningitidis ke haddasawa, kuma tana yaduwa ne ta hanyar numfashi musamman a wuraren cunkoson jama’a ko inda iska ba ta wadata. Hukumar ta…
Read More

Ba wanda ya isa ya cire mu – Iran kan barazanar Trump ta soke ƙasar a gasar Kofin Duniya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙasar Iran ta bayyana cewa babu wanda ya isa ya fitar da ita daga shiga gasar Kofin duniya da za a gudanar a ƙarshen wannan shekarar. Hakan wani mataki ne na martani da gargaɗi ga Shugaba Donald Trump na Amurka akan cewa “rayuwarsu da tsaronsu” na iya kasancewa cikin haɗari a Amurka, kamar yadda hukumomin Iran sika bayyana. Tawagar 'yan ƙwallon ƙafar ta Iran ta kuma bayyana a wani saƙo da ta wallafa a shafukan sada zumunta ranar Alhamis cewa, bai kamata a bar Amurka ta ɗauki baƙuncin gasar ba. A cewarta matuƙar ba…
Read More