22
Feb
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Victor Font ya jaddada aniyarsa ta dawo da Lionel Messi ƙungiyar Barcelona, inda ya ce ɗan Ajantinar ya cancanci samun bankawa mai cike da tsari a filin Camp Nou. A shekarar 2021 ne Messi ya bar Barcelona bayan da ƙungiyar ta gaza sabunta zamansa saboda ƙalubalen kuɗaɗe da ta fuskanta. Ganin haka ya sa zakaran ɗan ƙwallon duniyar ya koma Paris Saint-Germain, inda kuma daga bisani ya koma Inter Miami a Amurka da ke buga Gasar Major League Soccer. Duk da cewa ya bar Barcelona, Messi, wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or har sau…
