21
Feb
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar kula da Asusun Tallafa wa Yara Ƙanana na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ta sanar da cewa adadin yaran da aka yi wa rajistar haihuwa a Nijeriya acikin shekaru biyu da suka gabata ya ƙaru zuwa miliyan 14. Wakiliyar UNICEF a Nijeriya, Mis Wafaa Saeed Abdelatef ta bayyana haka a yayin wata ziyara ga Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, ranar Juma'a. Ta yaba wa Uwargidan bisa jagorancinta na ba iya inda UNICEF take aiki ba, har ma a wuraren da rayukan yara ƙanana da iyalai suke amfana…
