Babaji

5689 Posts

Sanatan Ribas Mpigi ya rasu a shekara 64

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sanata Barinada Mpigi da ke wakiltar santoriyar Ribas ta Kudu maso Gabas a Majalisar Dattawan Nijeriya ya rasu. Sanatan ya shefe kimanin sama da shekaru goma yana aiki a Majalisar Dokoki ta Ƙasa, sannan ya rasu yana da shekaru 64 a duniya. A ranar Alhamis, 19 ga Fabrairu, 2026 ne marigayin ya rasu a wani asibitin Landon bayan fama da wani gajeren rashin lafiya. Haka kuma ana kallon sa a matsayin na hannun daman Ministan Abuja Nyesom Wike. An haife shi ne a ranar 23 ga watan Yunin 1961. An fara zaɓen Mpigi a…
Read More

Zaɓen Abuja: Wike ya ayyana Juma’a a matsayin ranar hutu

Ministan Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ayyana Juma’a, 20 ga Fabrairu 2026, a matsayin ranar hutun aiki domin bai wa mazauna FCT damar shirin halartar zaɓen Ƙananan Hukumomi da za a gudanar a ranar Asabar, 21 ga Fabrairu. Haka kuma, Ministan ya sanar da takaita zirga-zirga a cikin Abuja daga karfe 8:00 na dare ranar Juma’a zuwa karfe 6:00 na yamma ranar Asabar. Ya umarci dukkan hukumomin tsaro da su tabbatar da bin wannan umarni yadda ya kamata. Wike ya yi kiran ne a wata sanarwa ta musamman ta hannun mataimakin sa na mussamman kan hudda da jama'a da…
Read More

Jami’an ICPC sun kai samame gidan El-Rufa’i na Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jami'an Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) sun kai samame gidan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da ke Abuja. Hakan ya biyo bayan kama shi da aka yi bayan Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta'annati (EFCC) ta bayar da belinsa. Rahotanni sun bayyana yadda jami'an ICPC suka kama El-Rufai bayan da EFCC jim-kaɗan bayan bada belin nasa a ranar Laraba. A daren Alhamis, Muyiwa Adekeye, mai magana da yawun El-Rufai, ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa an kai samame gidan tsohon gwamnan na Aso Drive. Rahotanni…
Read More

Samar da motocin sulke: Ministan Tsaro ya jinjina wa Gwamnan Zamfara kan jajircewa a fannin tsaro

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya yaba wa Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, bisa sayo motoci masu sulke, jiragen sa-ido marasa matuƙa (drones) da sauran kayan aiki domin ƙarfafa wa rundunonin tsaro a jihar. A wani biki da aka gudanar a Gidan Gwamnati da ke Gusau ranar Laraba, Gwamna Lawal ya miƙa motoci 25 na zamani masu sulke (Armoured Personnel Carriers) ga jami’an tsaro, domin ƙara musu kariya yayin da suke gudanar da aiki a yankunan da ke da haɗarin tsaro a faɗin jihar. Sanarwar da Kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya…
Read More

El-Rufa’i na komarmu bayan DSS ta ɗauke shi daga ofishin EFCC, inji ICPC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Yaƙi da Laifukan Rashawa da Makamantansu (ICPC) ta tabbatar da cewa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i na ƙarƙashin ikonta bisa binciken da ake yi akansa na wasu tuhume-tuhume da aka gabatar masa. A wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'arta, Mista J. Okor Odey ya fitar, ICPC ta ce El-Rufa'i yana hannunta har zuwa lokacin tashi a aiki na ranar 18 ga Fabrairu, 2026. Saidai hukumar ba ta yi ƙarin haske akan al'amarin binciken ba, amma ta tabbatar wa al'umma cewa za a bi hanyoyin da doka ta tanada wajen bayyana dukkan…
Read More

Filato: 30 sun rasu yayin da aka garzaya da 25 asibiti bayan fashewar gas a wajen haƙar ma’adinai

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Aƙalla masu aikin haƙar ma'adanai 30 ne suka rasu yayin da wasu guda 20 ke kwance a asibiti bayan shaƙar wata iska mai guba da ake zargin 'carbon monoxide' ce a wani wurin haƙar ma'adanai da ke Ƙaramar Hukumar Wase a Jihar Filato. Lamarin ya faru ne a ranar Talata wurin a wani ƙauye da ake kira Zuruk, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa manema labarai. Wani daga cikin mutanen ƙauyen ya ce masu haƙar ma'adanan na cikin rami a lokacin da hayaƙin gubar ya turnuƙe su, inda da dama daga cikinsu suka…
Read More

DSS ta yi ram da El-Rufa’i bayan barin hannun EFCC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yammacin Laraba ne jami'an Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, suka cafke Malam Nasir El-Rufa'i jim-kaɗan bayan ya bar hannun Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati (EFCC). Bayan kama shi ne, jami'an suka tsare shi, kamar yadda wata majiya mai ƙarfi ta shaida wa Blueprint.ng. Tsohon Gwamnan Jihar Kadunan na fuskantar sabon ƙalubalen ne bayan shafe kwana biyu a garƙame a hannun EFCC kamar yadda rahotanni suka bayyana. DSS ta kama shi ne bisa zargin yin kutse a wayar Mai bai wa Shugaban kasa Shawara akan Harkar Tsaro, Nuhu Ribaɗu. El-Rufa'i…
Read More

Tinubu ya sa hannu kan sabuwar dokar zaɓe

Shugab Bola Tinubu ya sanya hannu akan dokar zaɓen Nijeriya ta 2022 da aka yi wa gyaran fuska, yau Laraba. Hakan na zuwa ne kwana ɗaya bayan Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta amince da dokar bayan kwashe watanni ana tafka muhawara akanta. Gyaran dokar ya haifar da zazzafar muhawara a makon da ya gabata bayan wasu al'ummar ƙasar da kuma 'yan majalisa na jam'iyyar adawa suka nuna ƙin amincewa da ɓangaren dokar da ya yi magana akan tura sakamakon zaɓe. An riƙa taƙaddama akan matsayar da majalisar ta ɗauka na cewa za a iya amfani da takardar tura sakamakon zaɓe…
Read More

Zamfara: Gwamna Lawal ya ƙaddamar da manyan ayyuka a Ƙaramar Hukumar Anka

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sake jaddada ƙudirin sa na tabbatar da cewa jihar Zamfara ta shiga sahun jihohin da ke kan turbar ci gaba mai ɗorewa da amfanar al’umma baki ɗaya. A ranar Talata ne gwamnan ya ƙaddamar da manyan ayyukan raya ƙasa guda huɗu a Ƙaramar Hukumar Anka, a wani mataki da ke nuna cikar alƙawuran da ya ɗauka ga al’ummar yankin. A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ayyukan da aka ƙaddamar sun haɗa da sake gina da kuma cikakken gyaran fadar Sarkin Zamfaran Anka tare da saka kayan…
Read More

Kaduna: Kiristoci sun yabi Uba Sani bisa dawo da ɗaukar nauyin hajjinsu bayan shekara 11

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Al'ummar Kirista a Jihar Kaduna, sun yaba wa Gwamna Uba Sani na jihar bisa dawo da shirin ɗaukar nauyin hajjinsu bayan dakatar da shi na tsawon shekaru 11, inda suka bayyana hakan a matsayin ƙoƙarin tabbatar da adalci, daidaito da tsarin damawa da kowane ɓangare a gwamnatance. An yi wannan yabo ne a lokacin da ake wayar da kan mahajjan nasu na 2025 su guda 50, waɗanda gwamnatin jihar ta ɗauki nauyinsu. Wannan al'amari shi ne na farko tun tsawon sama da shekaru goma da gwamnatocin baya suka dakatar da shi. Tuni dai waɗanda…
Read More