18
Feb
A yau Laraba, tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i ya shafe kwana na biyu tsare a hannun Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati (EFCC) akan tuhumar almundahana, yayin da lauyansa, A.U Mustapha (SAN) ke fafutukar ganin an bada belinsa. Wasu alamu kuma na nuna cewa hukumar, na neman izinin ci gaba da tsare shi na wani lokaci, domin bashi damar amsa tambayoyin da ake masa. El-Rufa'i ya kai kansa hukumar ne ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairun 2026, da ƙarfe 10 na safe domin amsa tambayoyi kan zarginsa da almundahanar Naira biliyan 432. Kuma da zuwansa ofishin…
