17
Feb
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, ta sake buɗe shari'ar sanannen mai sharhi akan al'amuran gwamnati, Abubakar Idris da aka fi sani da Dadiyata, wanda ya yi ɓatan-dabo a Kaduna a shekarar 2019, da ɓatar wasu mutane da dama da aka alaƙanta su da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i. Wani babban jami'in tsaro ya bayyana haka, da kuma batun ƙwace fasfon El-Rufa'i a ranar Alhamis ɗin da ta gabata daga jami'an DSS a Filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja, inda ya ce an yi haka ne da nufin hana shi…
