
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Al’ummar Kirista a Jihar Kaduna, sun yaba wa Gwamna Uba Sani na jihar bisa dawo da shirin ɗaukar nauyin hajjinsu bayan dakatar da shi na tsawon shekaru 11, inda suka bayyana hakan a matsayin ƙoƙarin tabbatar da adalci, daidaito da tsarin damawa da kowane ɓangare a gwamnatance.
An yi wannan yabo ne a lokacin da ake wayar da kan mahajjan nasu na 2025 su guda 50, waɗanda gwamnatin jihar ta ɗauki nauyinsu.
Wannan al’amari shi ne na farko tun tsawon sama da shekaru goma da gwamnatocin baya suka dakatar da shi.
Tuni dai waɗanda suka samu amfana da shirin suka yi ta miƙa godiya ga gwamnan bisa farfaɗo da shirin, wanda a cewarsu, ya sabunta wa Kiristoci fata a jihar na jin cewa su ma ‘yan jiha masu cikakken ‘yanci.
Shugabar Ma’aikatar Ma’aikatan Kaduna, Misis Jimami C. Bako, ta yaba wa gwamnan bisa dawo shirin, inda ta ce gwamnatinsa tana martaba ci-gaban lamuran addini da duba masalaharsa al’umma da kuma ci-gaban tattali.
A cewar Kwamishinan Labarai, Ahmed Maiyaƙi, shirin wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin Uba Sani na tabbatar gaskiya da adalci ga ‘yan jihar.
