Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Biranen da za a fara da su sun haɗa da Katsina, Daura da Funtua kamar yadda gwamnan ya sanar a jawabinsa kafin ƙaddamar da shirin a ɗakin taro na masaukin shugaban ƙasa da ke cikin gidan gwamnatin jihar.
Ya ce tsara biranen har na tsawon shekara 14 zai haɗa da sauran ƙananan hukumomi 34 da ke jihar.
Malam Dikko ya bayyana cewa tun 1978 ba a sake tsari irin wannan ba wanda hakan yasa ake gine gine ba tsari.
“Musamman sabbin wurare da akayi gine gine zaka ga yawanci ba magudanan ruwa da fitar da layi layi da ababen hawa zasu wuce wanda haka ke kawo ambaliyar ruwa da rashin tsaro a waɗannan wurare.
Gwamnan sai yace wannan shiri na tsara birane zai sanya dole kafin wani ya sayi fili a ko ina ne ko ya kama hayan gida dole sai da sanin Mai Unguwa na wannan wurin.
“Mai Unguwa dole ya sanar da hukuma kafin mai saye ya mallaki filin ko a bashi hayan gida”,inji Dikko.
Haka kuma ya ce dole dillalin gidaje ya yi rajista da hukuma kafin ya cigaba da sana’ar ɗillancin gidaje ko bada hayar gida.
Gwamnan ya sanar da cewa har ya riga ya ya sanya hannu akan dokar da ta tanadi hukunci mai tsanani ga duk wanda ya karya wannan doka na mallakan fili da kama hayan gida.
Ya kuma nuna takaicin sa yadda a baya a kai ta ba mutanen da ba a sansu ba damar sayen gidaje da zama gidan haya ba tare da an tantance su ba haka ya sanya ake zaune da miyagun mutane ba a sani ba.
Yace gwamnatin sa ta riga ta fara aiwatar da tsarin a manyan biranen Katsina, Daura da Funtua ta hanyar gina manyan tagwayen hanyoyi da magudanan ruwa da samar da fitillu masu amfani da hasken rana a manyan hanyoyi da cikin unguwanni biranen.
