29
Jan
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyoyin ƙasar Ingila guda biyar sun yi nasarar hayewa zuwa zagaye na gaba a gasar kofin zakarun Nahiyar Turai daga zangon farko na kakar 2025/2026. Newcastle united ta shiga sahun waɗanda za su buga wasan ƙalubale gabanin zagayen 'yan 16, wato 'Play Offs'. Haka ma ƙungiyar Real Madrid, wadda ta lashe kofin har sau 15 a tarihinta, ta samu tsaiko na kai wa zangon kai-tsaye bayan da Benfica ta ƙasar Portugal da José Mourinho ke jagoranta ta lallasa ta da ci 4 da 2, inda mai tsaron gidanta Anatoliy Trubin ya zura ƙwallo ƙarshe…
