01
Feb
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa dukkan gwamnonin da aka zaɓa a ƙarƙashin inuwar APC, sune jagororin jam’iyyar a jihohinsu, yana mai jaddada tsarin jam’iyyar yayin sauye-sauyen jam'iyyun siyasa. Ya bayyana hakan ne a yayin taron karɓar Gwamna Agbu Kefas na Jihar Taraba zuwa APC da aka gudanar a Jalingo. Shugaban ya yi wannan bayani ta bakin Mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima, inda ya ce bisa ga sauya sheƙar Gwamna Kefas daga PDP zuwa APC, ya zama jagoran jam’iyyar APC a Taraba. Tinubu ya tabbatar da goyon bayansa ga gwamnan da gwamnatinsa domin kawo ci…
