Babaji

5689 Posts

NYEEF ta karrama Marigayi Uban Doman Gudu a taronta na 2026

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Inganta Rayukan Matasan Arewa da Wayar musu da Kai (NYEEF) ta karrrama Marigayi Alhaji Sulaiman Abubakar Uban Doman Gudu, wanda shi ne tsohon shugaban harkokin shugabancinta. A ranar 24 ga watan Junairu, 2026 NYEEF ta gudanar da taronta na shekara-shekara da ta saba yi a Kaduna, wanda ya haɗa manyan masana, malaman addinin, ƙwararru akan harkar tsaro. Haka kuma, akwai jagororin matasa da 'yan jaridu duk domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi arewacin Nijeriya da ma ƙasar baki ɗaya. A yayin haka ne ta yi jinjina ga marigayin, wanda ya yi aiki…
Read More

Juyin mulki: Har da ni aka shirya kashewa – Ministan Tsaro

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa Gwabin (mai ritaya) ya bayyana cewa yana ɗaya daga cikin mutanen aka hara a yunƙurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ba a yi nasara a kai ba. Ya ce, waɗanda suka kitsa makircin sun shirya kama shi sannan su harbe shi idan ya yi yunƙurin tirjewa. Janar Musa ya faɗi haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi, kwanaki kaɗan da aka tabbatar da shirin bayan kama wasu jami'an sojoji su guda 16 da hannu aciki a watan Oktoban 2025. Tsohon Babban…
Read More

Ɗan uwan Hadiza Bala Usman, Hussaini ya rasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mai taimaka wa Shugaba Bola Tinubu akan Tsare-tsare da Shirye-shirye, Hadiza Bala Usman ta shiga jimami a sakamakon rasuwar ƙaninta, Hussaini Bala Usman. A ranar Asabar marigayin ya rasu bayan fama da wani gajeren rashin lafiya, kamar yadda wata majiya ta iyalansu ta shaida wa manema labarai. A cewar majiyar, an gudanar da jana'izar Hussaini a yau Lahadi a Abuja kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Tun da misalin ƙarfe 1 na rana aka yi jana'izar a masallacin Juma'a na rukunin gidajen 'yan majalisar dokoki ta ƙasa da ke Zone 5. Wannan rashi ya…
Read More

Yadda Shettima ya ƙaddamar da shirin sake tsugunar da al’ummar Tudun Biri a Kaduna

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya ƙaddamar da shirin sake samar matsugunai ga al’ummar Tudun Biri da ke Ƙaramar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna, biyo bayan alkawarin da Shugaba Bola Tinubu ya yi na sake gina yankin bayan hatsarin jefa bom na soji bisa kure da ya faru shekaru biyu da suka gabata. Shirin ya ƙunshi gidaje guda 133 da aka kammala, cibiyoyin ilimi da sauran muhimman gine-gine na zamani, domin dawo da mutunci, kwanciyar hankali da rayuwa mai inganci ga al’ummar da abin ya shafa. Da yake jawabi yayin bikin kaddamarwar, Mataimakin Shugaban…
Read More

Iran ta ayyana sojojin Ƙungiyar Tarayyar Turai a matsayin ‘yan ta’adda

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Iran ta ayyana sojojin Tarayyar Turai (EU) a matsayin ƙungiyar ta'addanci kwanaki kaɗan bayan EU ta ayyana rundunar kare juyin juya halin ƙasar ta IRGC da ƙungiyar ta'addaci. Kakakin majalisar dokokin ƙasar ya sanar da haka a ranar Lahadi, bayan matakin da EU ta ɗauka na yin amfani da wannan sanarwar ga dakarun kare juyin juya halin Musuluncin ƙasar a 'yan kwanakin nan. An ga yadda yan majalisar suka sanya koren rigar masu gadi a wani nuni na haɗin kai a zaman majalisar inda suka yi ta rera taken "Mutuwa ga Amurka", "Mutuwa ga…
Read More

Atletico Madrid ta saye Ademola Lookman daga Atalanta

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗan wasan gaba na Super Eagles, Ademola Lookman ya kammala koma wa ƙungiyar Atletico Madrid, lamarin da ke nuna wa'adinsa a Atalanta da ke ƙasar Italiya ya zo ƙarshe. An yi musayar ɗan wasan ne akan kuɗi Yuro miliyan 40 bayan shafe tsawon makonni ana tattaunawa a tsakanin ƙungiyoyin biyu da kuma ɗan wasan. Atletico Madrid ta daɗe tana nuna kwaɗayin sayen ɗan wasan inda ta sha fuskantar gasa daga Fenerbahçe ta ƙasar Turkiyya, wadda da fari ya ƙulla amincewar baka da ita amma daga baya Atletico ta yi nasarar sayo shi. An samu…
Read More

Borno: Dakarun tsaro sun halaka Kwamandan Boko Haram, Abu Khalid a dajin Sambisa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dakarun Rundunar Sojojin Nijeriya sun yi nasarar kashe wani babban kwamandan mayaƙan ƙungiyar Boko Haram tare da wasu 'yan ta'adda a Dajin Sambisa. A cewar rahotanni, Abu Khalid, wanda shi ne maitaimakin shugaban mayaƙan, an halaka shi ne a wani atisayen shafewa da dakarun suka ƙaddamar a Arewa ta Gabas a ƙarshen mako. A cewar Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), majiyoyi sun ce Khalid, wanda jagora ne a harkokin gudanarwar ƙungiyar, kisan shi ya haifar da gagarumin giɓi ga ayyukan mayaƙan acikin maɓoyarsu da ke sanannen dajin. An gano cewa yana da hannu a kitsa…
Read More

‘Yan bindiga sun yi awon-gaba da mai shayarwa da mutane da dama a harin ƙauyukan Neja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja 'Yan bindiga a wani karon, sun sake kai farmaki a wasu ƙauyukan Ƙaramar Hukumar Agwara da ke Jihar Neja, inda suka ƙone ofishin 'yan sanda da coci, sannan daga bisani suka yi garkuwa da mai shayarwa da 'ya'yanta huɗu da kuma wasu mutane da ba a kai ga sanin adadinsu ba. An ruwaito cewa, sun kuma halaka wata tsohuwa a yankin Kabe, inda kuma suka yi awon-gaba da kayan abinci masu yawa a harin wanda suka ƙaddamar a safiyar ranar Lahadi. Haka kuma an gano cewa cocin da suka ƙona na Ɗarikar 'United Missionary…
Read More

Filato: ADP ta sake neman Sanata Pam Mwadkon Dachungyang ya yi murabus

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam’iyyar ADP a Jihar Filato, ta sake jaddada matsayarta cewa wajibi ne Sanata Pam Mwadkon Dachungyang ya bar kujerar Sanatan ta yankin Filato ta Arewa a nan take sakamakon ficewar da ya yi daga cikin jam’iyyar. ADP ta kuma bayyana ikirarin cewa akwai rikici a cikin jam'iyyar a matsayin ƙarya da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da jama'a da ba shi da tushe a tsarin mulki. A sanarwar da shugabancinta na ƙasa ya fitar a ranar Juma’a, ADP ta ce matsayin nata ya ta’allaka ne akan kundin tsarin mulkin ƙasa da aka yi wa…
Read More

Ribas: Nan gaba sai mun yi taronmu a filin wasa ko ba amincewar gwamnatin jiha – Wike

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ministan Abuja Nyesom Wike, ya yi barazanar cewa nan gaba za su shiga cikin Filin wasa na Yakubu Gowon da ƙarfi sakamakon zargin da ya yi wa gwamnatin jihar Ribas da hana jakadun Sabunta Fata shiga filin. Wike ya bayyana haka ne a ranar Juma’a yayin ƙaddamar da kodinetocin ƙungiyar na ƙananan hukumomi 23 da ke faɗin jihar. Ya ce, sun nemi a ba su damar gudanar da taron nasu a filin, amma gwamnatin jihar ta ƙi amince wa buƙatarsu, don haka ya ce nan gaba za su taro filin ko ba da amincewarta…
Read More