03
Feb
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A wani yunƙuri na neman kotu ta sake masa kadarorinsa da ta riƙe na wucin-gadi, Tsohon Antoni-Janar na ƙasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya shaida wa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja cewa ya samu miliyoyin kuɗaɗe daga albashi da alawus-alawus da kuma kyautaka a matsayinsa na jami'in gwamnati. Malami ya bayyana hakan ne yayin gabatar da sabon ƙorafi akan Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati (EFCC), wadda da fari ta samun izinin kotu na ƙwace kadarori guda 57 da aka alaƙanta su da Malami da 'ya'yansa biyu. Ya bayyana cewa…
