Babaji

5689 Posts

Tsohon shugaban gyaran fansho na ƙasa, Abdulrasheed Maina ya yanki jiki ya faɗi a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An garzaya da tsohon Shugaban Kwamitin Gyaran Fansho na ƙasa da aka mayar da shi Pension Reform Task Team a yanzu, wato Abdulrasheed Maina zuwa asibiti a ranar Talata sakamakon suma da ya yi a lokacin da yake ƙoƙarin shiga ofishinsa a Abuja. Rahotanni sun bayyana cewa al'amarin ya faru ne a safiyar ranar a lokacin da Maina ya fara jin jiri da rashin ƙarfin jiki, kana daga bisani ya yanki jiki ya faɗi ƙasa. Tuni ma’aikatan ofishin nasa suka garzaya da shi asibiti nan take domin ba shi agajin gaggawa. Mai taimaka masa…
Read More

Tsohon Gwamnan Benuwai, Gabriel Suswam ya koma APC bayan barin PDP

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Gwamnan Jihar Benuwai, Sanata Gabriel Torwua Suswam, ya fice daga Jam'iyyar PDP a hukumance, lamarin da ya kawo ƙarshen zamansa na tsawon lokaci acikinta bayan shafe shekaru da dama. Haka kuma ya sanar da komawarsa jam'iyya mai mulki, APC. Suswam, wanda ya shugabanci jihar Benuwai a tsakanin shekarar 2007 da 2015, sannan daga bisani ya yi sanata a Majalisar Dattawa, ya miƙa takardar murabusa ɗinsa daga PDP ga Shugaban jam'iyyar na yankin Mbagber da ke Ƙaramar Hukumar Logo a yau Laraba. A wata takarda da mai taimaka masa akan harkokin yaɗa labarai, Bartholomew…
Read More

Tinubu ya umarci Wike ya dakatar da yunƙurin tsige Gwamnan Ribas

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya umarci Ministan Abuja Nyesom Wike da ya dakata da shirin tsige Gwamnan Jihar, Ribas Siminalayi Fubara. A ranar 8 ga watan Junairu ne majalisar dokokin jihar ta fara shirin tsige Fubara da Mataimakiyarsa, Ngozi Odu bisa zargin su da saɓa wa ƙa'idar aiki. Wannan shi ne karo na uku da 'yan majalisar suke yunƙurin tsige gwamnan tun bayan zaɓar sa a 2023. Hakan na zuwa ne jim-kaɗan bayan Wike ya zargi Fubara da karya alƙawarin sulhu da Shugaba Tinubu ya jagoranta a tsakaninsu tun a watan Yunin 2025 a lokacin…
Read More

Trump ya tura wa Nijeriya sojoji don magance matsalar tsaro

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Amurka ƙarƙashin jagorancin Donald Trump, ta tura wani ƙaramin rukunin sojoji zuwa Nijeriya. Babban Janar da ke kula da rundunar sojin Amurka a Afirka (AFRICOM), Dagvin R.M. Anderson ya bayyana a ranar Talata. Wannan shi ne karon farko da aka tabbatar da kasancewar sojojin Amurka a Nijeriya tun bayan da Washington ta kai hare-haren sama a ranar Kirsimeti. Shugaban Amurka Donald Trump ya bayar da umarnin kai hare-haren sama kan abin da ya bayyana a matsayin wuraren da ’yan kungiyar Islamic State ke amfani da su a Nijeriya a watan Disamba, inda ya…
Read More

EFCC ta cafke jarumar Kanywood, Samha Inuwa kan zargin wulaƙanta Naira

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati (EFCC) yaƙi ta kama jarumar Kannywood, Samha M Inuwa bisa zargin ta da ayyukan wulaƙanta takardar naira. A sanarwar da EFCC ta wallafa a shafinta na X, ta ce ta kama Samha ne a jiya Talata bayan samun wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta da ya nuna yadda take share majina da takardar kuɗi na N1,000. A cewarta, hakan ya sanya ta gaggauta kama Samha bayan fitar bidiyon, inda aka cafke ta don ta je ta amsa tambayoyi. EFCC ta ƙara da cewa, a…
Read More

Kano: Za a riƙa yi wa ‘yan ƙasa rajistar zaɓe a inda suke – Baturen zaɓe

Hukumar Zaɓe a Jihar Kano ta sahale a yi wa kowane ɗan kasa rijistar zaɓe a mazaɓarsa domin sauƙaƙa wa al'umma damar mallakar katin zaɓensu. Baturen zaɓe na Karamar Hukumar Bichi, Alhaji Abdur-Rahman Haruna Rafin-Dadi ne ya bayyana haka, yayin tattaunawarsu da Jami'ar Yada Labaran ƙaramar hukumar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo. Alhaji Abdur-Rahman Haruna ya ce, an koma gudanar da rijistar a dukkan mazabu a halin yanzu. "An mayar da yin rijistar zabe daga ofishin Hukumar Zabe na Bichi zuwa kowace mazaba." Baturen Zabe na Karamar Hukumar Bichi, Alhaji Abdur-Rahman Haruna Rafin-Dadi. Kazalika, aikin gudanar da rijistar zaben zai tafi…
Read More

‘Yan bindiga sun halaka ɗan Marigayi Gaddafi, Saif al-Islam a Libiya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rahotanni daga ƙasar Libiya sun nuna cewa wasu da ake zargin 'yan bindiga ne, sun halaka Saif al-Islam Gaddafi, wanda ɗan tsohon shugaban ƙasar Marigayi Muammar Gaddafi ne. A cewar Al Jazeera ana ganin an harbe Saif al-Islam ne a yankin Zintan da ke Yammacin Libiya inda a nan yake zaune tsawon shekaru da dama. Kawo yanzu dai ba a san musabbabin kashe Saif al-Islam ba. Wata 'yar uwarsa ta shaida wa gidan talabijin na ƙasar cewa ya mutu ne a kusa da iyaƙar ƙasar da Aljeriya, ba tare da bayyana ta yadda ya…
Read More

Zargin sauya akalar kuɗaɗe: Kotu ta ayyana 15 ga Afrilu a matsayin ranar shari’ar Ganduje da matarsa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wata Babbar Kotu a Jihar Kano, ta sanya ranar 15 ga watan Afrilu, 2026 a matsayin lokacin da za ta yi hukunci akan shari'ar da ake tuhumar tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da wasu da hannu a sauya akalar wasu kuɗaɗe. Ana tuhumar Ganduje da matarsa tare da wasu mutane da kamfanoni da hannu a laifuka 11 da suka haɗa da karɓar rashawa, haɗin baki, almundahana da karkatar da kuɗaɗen gwamnati da suka kai biliyoyin naira. Sauran sune: Abubakar Bawuro, Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Ltd, Safari Textiles Ltd, da kuma Lasage…
Read More

DSS ta gurfanar da Malami da ɗansa a kotu kan zargin ɗaukar nauyin ta’addanci

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yau Talata ne Hukumar Tsaro ta Farin kaya (DSS) ta gurfanar da tsohon Ministan Shari’a kuma Antoni-Janar na Ƙasa, Abubakar Malami (SAN) tare da ɗansa a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa zargin su da ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci. An gurfanar da waɗanda ake tuhumar ne a gaban Mai Shari'a Joyce Abdulmalik, inda suka musanta hannu a laifuka biyar masu alaƙa da ta'addanci da DSS ɗin ta gabatar akansu. A cewar takardar ƙorafin, ana zargin Malami da ɗaukar nauyin ta’addanci a lokacin da yake riƙe da muƙamin babban lauya na ƙasa…
Read More

NECO: Kaso 80 sun yi nasara a sakamakon jarrabawar 2025

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Jarrabawa ta Kasa (NECO) ta sanar da fitar da sakamakon jarrabawar SSCE na ɗalibai na musamman, wato 'External' na 2025, inda ta bayyana cewa sama da kashi 80 na ɗaliban da suka rubuta ta sun samu aƙalla kiredit biyar zuwa sama. Rijistara kuma Shugaban hukumar, Farfesa Ɗantani Wushishi a wata hira da manema labarai a hedikwatar NECO da ke Minna a Jihar Neja, ya ce an kammala tantance sakamakon cikin nasara kuma tuni aka ɗora su a shafin hukumar domin dubawa. Ya bayyana cewa, jimillar ɗalibai 96,979 ne suka yi rajista, yayin da…
Read More