06
Feb
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi (MWL) ta yi alla-wadai da harin 'yan ta'adda da ya yi sanadiyyar mutuwar mazauna garin Woro a Jihar Kwara, inda aka yi wa mutane da dama kisan gilla da raunata wasu. A wata takarda da ta fitar a Babbar Sakatariyarta da ke Makka, MWL ta bayyana harin a matsayin mummunan ta'addanci ga al'ummar musulmi, tana mai tir da nuna ƙiyayyarta ga dukkan ayyukan ta'addanci a sassan Nijeriya. MWL ta ce tana tare da Nijeriya a wannan lokaci na alhini tare da goyon bayanta akan ƙoƙarin da take yi wajen magance matsalolin…
