Babaji

5689 Posts

An maye gurbin tutocin NNPP da na APC a gidan gwamnatin Kano

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gidan gwamnatin jihar Kano ya ɗauki sabon salon siyasa yayin da aka cire tutocin jam'iyyar NNPP tare da maye gurabensu da na APC mai mulki, lamarin da ke nuna an samu sabon sauyi a karon farko tun bayan kama mulkin Gwamna Abba Kabir Yusuf. Hakan na zuwa ne yayin da ake shirin tarbar gwamna zuwa cikin jam’iyyar APC a hukumance a yau Litinin. Rahotanni sun nuna cewa an kawata harabar gidan gwamnatin da launuka da tutocin APC, lamarin da ya ƙara jawo hankalin jama’a gabanin taron da za a gudanar domin sanar da sauyin.…
Read More

‘Yan sanda sun kama tirela maƙare da ababen fashewa a Oyo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar 'yan sanda a Jihar Oyo, ta ce jami'anta sun ti nasarar kama wata tirela mai maƙare da ababen fashewa a yankin Saki da ke jihar. A cewar wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'arta, DSP Olayinka Ayanlade ya fitar, an cafke motar ne a wani shigen bincike yayin da jami'an suke bakin aiki. Ya ce, tuni aka garzaya da motar da ababen fashewar zuwa ofishin jami'an, waɗanda ake cigaba da gudanar da bincike akansu. Jami'in ya ƙara da cewa an yi nasarar kamen ne sakamakon samun wani bayani na sirri, inda bayan haka…
Read More

Zargin juyin mulki: Rundunar soji ta miƙa wa Tinubu rahoton bincike

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar Sojoji ta miƙa wa Shugaba Bola Tinubu rahoton binciken da ta gudanar akan wasu jami’anta da aka zarga da yi wa gwamnatinsa yunƙurin juyin mulki. Hukumar Leƙen Asiri ta rundunar (DIA) ta miƙa rahoton ne wata biyu bayan tsare wasu hafsoshin soji 16, da ake zargi da yunƙurin juyin mulkin ciki har da wani mai muƙamin Birgediya Janar. Wasu manyan hafsoshin soji masu kusanci da binciken sun shaida wa manema labarai cewa, sakamakon binciken ya samu sojojin da ake zargi da laifin yunƙurin kifar da gwamnati, kamar yadda aka tuhume su. A cewarsu,…
Read More

Gwamnan Kano zai koma APC yau

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf zai koma jam'iyyar APC, mai mulki a yau Litinin, 26 ga watan Janairu, 2026. A ranar Juma'a ne gwamnan ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar NNPP, saboda abin da ya bayyana da rikicin cikin gida da ke addabar jam'iyyar, sai dai a lokacin bai bayyana jam'iyyar da zai shiga ba. A sanarwar da kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Lahadi, ya ce gwamna ya yanke shawarar komawa tsahowar jam'iyyarsa ta APC bayan tuntuɓar abokan shawararsa na siyasa da sauran masu ruwa da tsaki. Gwamnan ya bayyana APC da jam'iyya mai…
Read More

Kano: Kwamishina ya yi murabus yayin da ɗan Kwankwaso ke neman ajiye muƙaminsa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kwamishinan Kimiyya, Fasaha da Ƙirƙire-ƙirƙire na Jihar Kano, Yusuf Ƙofar Mata ya ajiye muƙaminsa na kwamishina, inda ya ce matakin ya biyo bayan sauye-sauyen siyasa da suka kauce wa tsarin da aka gina gwamnatin a kansa. Yusuf Ƙofar Mata ya sanar da hakan ne ta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, inda ya ce ya yanke shawarar ne domin bin ƙa’ida da akidar siyasar da aka kafa gwamnatin Kano mai ci a kai. Ya kuma nuna godiyarsa ga Allah Maɗaukakin Sarki, sannan ya miƙa godiya ta musamman…
Read More

Sojoji sun kama tsohuwa kan samar wa ‘yan ta’adda ƙwayoyi a Borno

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dakarun tsaro a shiyyar Arewa ta Gabas da ke aiki a ƙarƙashin tawagar Atisayen Haɗin Kai (OPHK), sun yi wata gagarumar nasara a ƙoƙarinsu na daƙile ayyukan tallafa wa ta'addanci a yankin. A cewar wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na jami'an haɗaka na OPHK, Laftanal Kanal Sani Uba ya fitar a yau Lahadi, jami'an sun yi nasarar kama wata tsohuwa mai suna Hauwa Abdlazeez 'yar kimamin shekara 65 a ranar 23 ga watan Junairu, 2026. An kama matar, wadda ake zargin ta da yi wa 'yan ta'adda dillancin miyagun ƙwayoyi ne a…
Read More

Ayyuka: Babu ƙaramar hukumar da aka bari a baya – Gwamnatin Kaduna

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya ce gwamnatinsa tana gina titina guda 140 a baki ɗaya ƙananan hukumomi 23 da ke faɗin jihar, waɗanda jimillar tsawonsu ya kai kilomita 1,335. Ya bayyana cewa, gwamnatin a halin yanzu ta fara aikin kowannensu, yana mai ƙarawa da alƙawarin kammala ayyukan da ya gada daga gwamnatocin baya. Uba Sani ya faɗi haka ne a jiya Asabar, a lokacin da yake ƙaddamar da titin asphalt da ya haɗa Durum zuwa Kuruntumawa a Ƙaramar Hukumar Maƙarfi, inda ya ce dukkan ayyukan titinan ana gudanar da su bisa inganci.…
Read More

Kwankwaso ya ayyana 23 ga Junairu a matsayin ranar butulci kan barin Abba NNPP

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon ɗan takarar shugaban kuma jagoran Jam'iyyar NNPP, Rabi'u Musa Kwankwaso, ya ayyana 23 ga watan Junairu a matsayin "ranar butulci" bayan da Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya fice daga jam'iyyar akan raɗe-raɗin komawarsa APC mai mulki. Kwankwaso ya bayyana haka ne a ranar Juma’a yayin gabatar da jawabi ga magoya bayansa a Kano jim-kaɗan bayan Gwamna Abba ya bar NNPP a hukumance. Ya bayyana ranar a matsayin lokaci na dindindin na tuni ga karya alƙawari da butulci a siyasa bisa la'akari da matakin gwamnan, wanda masu sha akan harkokin siyasa…
Read More

‘Yar Ganduje ta kammala karatu a Kwalejin King’s da ke Landon

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Shugaban Jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya yi murnar kammala karatun 'yarsa Fatima a Kwalejin King's da ke Landon. Rahotanni sun bayyana cewa, Fatima ta kammala karatun digiri na biyu, wato digirin digir a King’s College London da ke Birtaniya. Tsohon gwamnan ya wallafa hakan a wani bidiyo da ke nuna shi cikin farin ciki yana rungumar ‘yarsa sanye da rigar kammala karatu, kafin ya miƙa mata furanni domin taya ta murna. A cikin sakon da ya rubuta tare da bidiyon, Ganduje ya yaba wa Fatima bisa jajircewarta, ladabi da kuma…
Read More

Jigawa: Ta yi ajalin mijinta da maganin ɓera don ba ta son shi

Rundunar 'yan sanda a Jihar Jigawa, ta tabbatar da kama wata amarya bisa zargin kashe angonta makoni bayan aurensu. Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Lawal Shi'isu Adama ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne a ƙauyen Guaza da ke yankin Ƙaramar Hukumar Jahun, bayan da aka zargi matar da amfani a shinkafar ɓera (guba) wajen kashe mijin nata. Bayanan farko da 'yan sanda suka samu sun nuna cewa angon ya ci abincinsa na rana a gida daga nan ya fara jinya, lamarin da ya a aka gaggauta kai shi asibiti, inda likitoci suka tabbatar…
Read More