Babaji

5689 Posts

Shettima ya koma Abuja daga taron tattali a Switzerland

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya koma Abuja bayan balaguron da ya yi inda ya shafe mako guda yana gudanar da harkokin difulomasiyya da tattalin arziƙi a ƙasashen Guinea-Conakry da Switzerland. Wata sanarwa da mai taimaka masa akan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha ya fitar, ta ce mataimakin shugaban ƙasar ya isa filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe ranar Asabar. Shettima ya wakilci Shugaba Bola Tinubu a wajen bikin rantsar da shugaban ƙasar Guinea, Mamadi Doumbouya, ya kuma jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron tattalin arziki na duniya (WEF) karo na 56 a Davos. Da farko dai Shettima ya ziyarci birnin Conakry,…
Read More

Kisan Kurmin Wali: An yaba wa Gwamna Uba Sani bisa ziyartar jama’ar ƙauyen

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An yaba wa Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna bisa zuwa ƙauyen Kurmin Wali domin jajenta wa al'ummar yankin bisa garkuwa da mutanensu da 'yan bindiga suka yi a ranar Lahadin da ta gabata. Wasu daga cikin waɗanda suka tsere a yayin faruwar al'amarin ne suka yi jinjinar a ranar Juma'a inda suka jaddada goyon bayansu ga jagorancin gwamnan bisa ziyarar da kuma ba su kulawar lafiya da fadakar da su akan al'amuran yau da kullum. Da yake ganawa da manema labarai, Mista Joseph Kurmin Wali ya bayyana yadda maharan siak farmake su a…
Read More

Matashi ya yi ajalin matar aure a Zamfara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wani matashi mai suna Hassan Ɗan Canji ya yi sanadiyyar mutuwar wata Rakiya, wadda iyalin wani Malam Maikuɗi ce da ke Ƙauyen Dambo a Ƙaramar Hukumar Bakura ta Jihar Zamfara. Wani mazaunin yankin, Malam Tukur Dambo ya shaida wa manema a wata hira ta waya cewa al'amarin ya auku ne a daren ranar Alhamis wayewar Juma'a bayan matashin ya yi hatsaniya da matar. "Bayan hatsaniyar, sai ya shiga gida ya ɗauko adda, sannan ya daɓa mata har lahira", inji shi. A cewar mazaunin, ganin haka ke da wuya, 'yan uwar matar suka mayar da…
Read More

Ribas: APC ta yaba wa Fadar Shugaban Ƙasa kan jaddada Fubara a matsayin jagoran jam’iyyar a jihar

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam'iyyar APC a Jihar Ribas, ta yaba wa matakin fadar shugaban ƙasa na jaddada Gwamna Siminalayi Fubara a matsayin jagoran jam'iyyar a jihar, tana mai cewa hakan ya fito da ainihin matsayar jam'iyyar a jihar. APC ta kuma nuna godiya matuƙa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa tsayuwa tsayin daka akan dokokin jam'iyyar wajen jaddada matsayin gwamnan ta mai taimaka masa akan tsare-tsaren sadawa, Danie Bwala. A sanarwar da APC a Jihar ta fitarta hannun Kakakinta, Darlington Nwauju a ranar Juma'a, jam'iyyar ta ce hakan da fadar ta yi ya nuna haƙiƙanin matsayar APC…
Read More

‘Ni ba na sayerwa ba ne’: Kwankwaso ya magantu bayan Abba ya bar NNPP

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabi'u Musa Kwankwaso, ya sake jaddada cewa ba zai taɓa sayar da kyawawan manufofinsa na siyasa ba domin riba ta ƙashin kansa. Kwankwaso ya bayyana haka ne sa'o'i da yaronsa na siyasa kuma Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da ciyamomi da 'yan majalisar dokokin jihar da ta tarayya suka sanar da ficewarsu daga jam'iyyar. Tsohon gwamnan na Kano ya faɗi haka ne a yayin jawabi ga magoya bayansa a gidansa da ke Kano, inda ya ce tsawon lokaci da ya ɗauka…
Read More

Arbeloa ya shawarci Alexander-Arnold ya bar Madrid bayan cire shi a shirinsa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sabon mai horar da 'yan wasan Real Madrid, Alvaro Arbeloa ya bayyana aniyarsa ta cigaba da jan ragamar ƙungiyar a kakar wasa ta gaba. A cewar wani rahoto da El Nacional ta fitar, Arbeloa ya kuma shawarci ɗan wasan baya, Alexander-Arnold na ƙasar Ingila da ya shirya barin ƙungiyar kasancewar ba ya daga cikin 'yan wasan da kocin yake shirin tafiya da su. Haka na zuwa ne ƙasa da kwanaki 14 da Arbeloa ya kama jagorancin ƙungiyar bayan Madrid ta sallami Xabi Alonso a muƙamin. Duk da cewa da fari ana ganin naɗin Arbeloa…
Read More

2026 OSCAR: Hollywood ta fitar da jaddawalin finafinan da ka iya lashe kyautar

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Masana'antar shirya finafinan Hollywood ta sanar da fitar da jaddawalin finafinan da ka iya samun lambar yabo ta OSCAR bisa ayyukansu na shekarar da ta gabata. Wani fim mai suna "Sinners" tuni ya samu karɓuwa a sahun waɗanda suka yi fice inda aka zaɓe shi har sau 16, lamarin da ke nuna ya kere finafinai kamar su All About Eve (1950), Titanic (1997) da La La Land (2016). Baya da shi akwai One Battle After Another da aka zaɓa sau 13, sai kuma Marty Supreme, Frankenstein da Sentimental Value da aka zaɓi kowannensu sau…
Read More

Amurka ta fice daga WHO a hukumance

FILE - President-elect Donald Trump speaks during a meeting with the House GOP conference, Nov. 13, 2024, in Washington. (Allison Robbert/Pool via AP, File) Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Amurka ta sanar da kammala ficewa daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a hukumance, inda ta ce ɗauki matakin ne bisa la'akari da rashin kula da annobar COVID-19 yadda ya dace, rashin gyara da sanya siyasa daga ɓangaren ƙasashen da ke ƙarƙashin hukumar. Wannan mataki ya fara aiki ne daga 22 ga Janairun 2026 bayan cika sharaɗin sanarwar shekara guda. Sakataren Harkokin Wajen ƙasar, Marco Rubio da Sakataren Lafiya Robert…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnan Kano ya bar NNPP

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP, matakin da ya danganta da tsanantar rikice-rikicen cikin gida a jam’iyyar da kuma buƙatar kare muradun al’ummar jihar Kano gaba ɗaya. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Juma’a. A cikin wasiƙar da ya aike wa Shugaban mazabar Diso-Chiranchi na jam’iyyar NNPP a Ƙaramar Hukumar Gwale, gwamnan ya sanar da janyewarsa daga jam’iyyar, wanda zai fara aiki daga ranar Juma’a, 23 ga Janairu, 2026. “Ina rubuta wannan…
Read More

Op-Ed: Sauyin jin ƙai a Nijeriya zai yi nasara idan jagorancin ƙananan hukumomi ya ɗauki matakin gaba

Daga MOHAMED MALICK FALL da Dakta BERNARD M. DORO Nijeriya na cikin sabon lokaci na musamman a tafiyar tallafin jin kai. Nijeriya tana fuskantar wani yanayi mai tsauri a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashe takwas da ke cikin sauyin tsarin agajin jin kai na duniya: Buƙatun jin ƙai suna cigaba da ƙaruwa, yayin da tallafin duniya ke raguwa sosai.Wannan rikicin na tilasta muhawara kan yadda ake isar da tallafin jin kai — kuma muhimmansa, wanene ke jagorantar ta. Ƙalubalen nan sun fi bayyanawa a yankin arewa maso gabashin Najeriya, inda bukatun jin kai suka fi tsanani kuma matsalolin tsaro da…
Read More