16
Feb
Daga BELLO A. BABAJI Gwamna Uba Sani na Kaduna ya tabbatar wa jigajigan APC 50 da suka dawo jam'iyyar cewa za su mori amfanin zamansu acikinta kamar kowane ɗan jam'iyya. Sanannu daga cikin waɗanda suka sauya sheƙar sun haɗa da tsohon gwamnan jihar, Muktar Ramalan Yero; Sanata Shehu Sani; tsohon ɗan takarar gwamnan jihar a jami'yyar NNPP, Sanata Suleiman Hunƙuyi; da tsohon ɗan takarar gwamnan jihar, Alhaji Sani Sha'aban. Sauran sun haɗa da, Sanata Ɗanjuma Laah, Abubakar Mustapha da kuma Ambasada Sule Buba. Gwamna Uba Sani ya bayyana jin-daɗinsa ga cigaban da jam'iyyar ta samu, ya na mai cewa babu…
