17
Feb
Daga BELLO A. BABAJI An harbe wani babban malami da ya shahara a harkar luwaɗi mai suna Muhsin Hendricks a ƙasar Afirka ta Kudu, bayan jagorantar wani auren jinsi na ƴan maɗigo. Hendricks mai shekaru 57, mutum ne da ya samar tare da jagorantar wani masallaci a Cape Town musamman don musulman da aka mayar da su saniyar ware waɗanda daga ciki akwai ƴan auren jinsi, wato 'LGBTQ+ Community'. A safiyar ranar Asabar ne aka kashe limamin a lokacin da ya ke tafiya zuwa wani gari a wata mota a birnin Gqeberha dake Kudancin ƙasar. Ana zargin cewa an harbe…
