19
Feb
Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da barikin Hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi (NDLEA) a Yola, Jihar Adamawa, wanda kuma shi ne na farko a Nijeriya. Shugaban NDLEA, Mohamed Buba Marwa (rtd), ya ce barikin zai taimaka wajen bunƙasa ayyukan jami'ansu wajen yaƙin da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Nijeriya. Ya ce, rashin bariki a baya ya sanya jami'an hukumar da iyalansu faɗawa cikin haɗurra. An buɗe barikin ne, wanda ke unguwar Kwanan Waya, da ke da faɗin Hekta 18 ga jami'an NDLEA da iyalansu, wanda kuma aciki akwai ofsoshi, gidajen jami'a da wuraren nazarin…
