Babaji

5706 Posts

An rufe Jami’ar Tarayya ta Lokoja

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Gudanarwar Jami'ar Lokoja ta Jihar Kogi ta sanar da rufe makarantar, biyo bayan mutuwar ɗalibai guda biyar a yayin wani hatsari. A ranar Litinin ne Rajistirar Jami'ar, Dakta Rebecca Aimiohu Okojie ta bayyana hakan a wata takarda da fitar, inda ta zayyano kwamishinan ƴan sandan jihar da daraktan Hukumar DSS aciki. Haka kuma a ranar ta Litinin, 17 ga watan Fabrairu ne wani hatsarin tirela ya yi sanadin mutuwar ɗaliban jami'ar biyar a Birnin Felele. Lamarin da ya harzuƙa sauran ɗaliban, inda suka yi gangami a ƙofofin jami'ar duk cewa gwamnatin jihar da Hukumar gudanarwar…
Read More

Ruftawar ginin makaranta ta hallaka mutum ɗaya da jikkata wasu a Yobe

Daga BELLO A. BABAJI Mutum ɗaya ya rasa ransa yayin da wasu huɗu suka samu raunuka a lokacin da wani gini ya rushe a wata makarantar kwalejin mata ta GGTC Potiskum dake Jihar Yobe. Tuni aka garzaya da sauran mutane huɗun da suka jikkata zuwa asibiti don ba su kulawa. Blueprint ta ruwaito cewa, lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 12 na rana a lokacin da ake tsaka da ɗaukar darussa a wani sashi na ginin ɗakunan karatu guda biyu na ƴan aji biyu a babbar sekandire, wato SS2. Kowane ɗaya daga cikin ajujuwan na ɗaukar ɗalibai 25 inda…
Read More

CBD ya umarci bankuna su wallafa asusun da aka rufe da kuɗaɗen da ba a neme su ba

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya umarci bankuna da sauran cibiyoyin kuɗaɗe da su bayyana wa al'umma asusun da aka rufe da kuɗaɗen da aka bar su kara zube da wasu kadarorin kuɗi a shafukan yanar gizo. Hakan na ƙunshe ne a wata takarda ɗauke da sanya hannun jami'i Michael Akuka a madadin Daraktan Ɓangaren Tsare-tsaren Kuɗi da gudanar da su na bankin. Umarnin ya buƙaci cibiyoyin kuɗaɗen da su wallafa sunayen mutanen da ke da asusun da aka rufe da irin asusun da kuma wajen da aka buɗe asusun. Ya ce, yayin da aka…
Read More

Gwamnatin Katsina ta ware Naira biliyan 2.3 don ciyarwa a Ramadan

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Kwamishinan Noma na jihar, Farfesa Ahmed Muhammad Bakori ya faɗa wa manema labarai haka bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dikko Raɗɗa. Ya ce kuɗin da gwamnatin ta ware za ta sayi nau'ukan hatsi da suka haɗa da shinkafa da masara domin raba wa marasa ƙarfi da masu nisan shekaru kyauta a lokacin azumin watan Ramadan. Bakori ya ƙara da cewa gwamnati tana gudanar da wannan shiri a kowacce shekara domin sauƙaƙa wa al'ummar musulmi su gudanar da ibadu cikin nitsuwa. "Za a raba kayan abincin gida biyu; Kashi guda a…
Read More

Yanzu-yanzu: Shugaban sojojin ƙasa ya je Zamfara

Daga BELLO A. BABAJI Jagoran sojojin ƙasa (COAS) Laftanal Janar Olufemi Oluyede yana Gusau, babban birnin jihar Zamfara a halin yanzu, a wata ziyara ta kwana ɗaya. A yayin ziyarar ne zai gana da tawagar atisayen 'Fansan Yamma', ƙarƙarshin jagorancin shugabanta, wato Manjo-Janar Oluyinka Soyele. Blueprint ta ruwaito cewa, babban jami'in zai kuma ziyarci hedikwatar Birget ta ɗaya ta rundunar dake Gusau da rukunin 'Garrison Cantonment', inda zai gabatar da jawabi ga dakarun. Zamfara na ɗaya daga cikin jihohin da ke fama da matsanancin rashin tsaro sakamakon ayyukan ƴan bindiga tsawon sama da shekaru goma.
Read More

An sako tsohon shugaban ma’aikatan gwamnatin El-Rufa’i bayan kwanaki 50 a tsare

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon shugaban mai'aikatan gwamnatin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, Bashir Sa'idu ya fito daga hannun hukuma, bayan tsare shi da aka yi na tsawon kwanaki 50 kan zargin sa da hannu a almundahana. El-Rufa'i ya bayyana hakan ta kafar X a ranar Laraba, inda ya bayyana tsare shi a matsayin abinda aka yi ba bisa adalci ba da kuma siyasantar da lamarin. Ya ce, Bashir Sa'idu abokinsa ne na tsawon sama da shekaru 53, wanda kuma sun yi karatu a Kwalejin Barewa ta Zariya tare kuma tsohon kwamishinan ƙananan hukumomi da kuɗi. El-Rufa'i ya…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta maka Binance a kotu kan asarar Dala biliyan 81.5

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Tarayya ta maka Kamfanin Binance Holdings Limited a Babbar Kotun Tarayya don neman a biya ta Dala biliyan 79.51 da Naira miliyan 231 bisa zargin kamfanin da haddasa mata asara. Haka kuma a cikin ƙarar, Hukumar Tattara Haraji ta Ƙasa (FIRS) ta nemi kotun da ta tilasta kamfanin ya biya Dala biliyan 2.001 na harajin shekarun 2022 da 2023. Hallau FIRS ta ce, manyan jami'an kamfanin biyu, wato Trigram Gambaryan da Nadeem Anjarwalla sun haddasa wa tattalin arziƙin Nijeriya asara sakamakon rashin yin rajista da hukumar. An shigar da Binance ƙara ne sakamakon aikata laifukan…
Read More

Abin fashewa ya yi sanadin mutuwar mutum biyu a wata kasuwa a Zamfara

Daga BELLO A. BABAJI Mutane biyu ne suka rasa rayukansu a yayin da wata hodar bindiga ta tarwatse a wata kasuwar ƙauye dake ƙaramar hukumar Talata-Mafara a jihar Zamfara. Lamarin ya faru ne a ranar Talata, wanda ya jafe ƴan tireda da masu shaguna cikin firgici tare da guje-guje domin neman tsira. Wani mutum ya shaida wa manema labarai cewa abin fashewar ya tarwatse ne a wani shago da ake harkar bindigun gargajiya. Ciyaman ɗin ƙaramar hukumar, Yahaya Yari ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce tuni aka garzaya da waɗanda suka samu raunuka zuwa Asibitin Koyarwa na Usman…
Read More

Karɓe ikon ƙananan hukumomi cin amanar ƙasa ne – Gargaɗin Ministan Shari’a ga gwamnoni

Daga BELLO A. BABAJI Antoni-Janar na Ƙasa kuma Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi ya bayyana karɓe iko ba bisa doka ba na ƙananan hukumomi da gwamnoni ke yi a matsayin cin amanar ƙasa. Antonin ya faɗi hakan ne a yayin wani taro da Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) ta shirya a Abuja, ranar Laraba. Fagbemi, wanda Daraktan ofishin ɗaukaka ƙara na Ma'aikatar Shari'a, Tijani Gazali ya wakilce shi, ya ce duk da hukuncin Kotun Ƙoli na ba su ƴancin cin gashin kai da dokokin da ke hana shiga harkokinsu, wasu gwamnoni da majalisun dokokinsu suna cigaba da juya lamuran zaɓaɓɓun ciyamomi ba…
Read More

Majalisar Malaman Kano ta sasanta rikicin Masallacin Sahaba

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano A ƙarshe dai Majalisar Malaman Jihar Kano ta cimma matsaya akan dambarwar Masallacin Jumma'a na Sahaba, dake Kundila a jihar. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Shugaban Majalisar, Sheikh Malam Ibrahim Khalil, wanda ya ce bayan zama da dukkanin ɓangarorin masallacin ne, majalisar ta yanke hukunci na ƙarshe akan rikicin. Ya ce, sun yanke hukuncin cewa Sheikh Muhammad Bin Othman zai koma masallacin, yayin da Mai Kifi da sauran mutanensa kuwa za su cigaba da riƙe nasu masallacin na Jami’urrahman. Malam Ibrahim Khalil ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke bayyana sakamakon…
Read More