Babaji

5706 Posts

Dalilan sirri ne – Martanin Ƙasar Kanada bisa ƙin bada biza ga jagororin tsaron Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI Babbar Hukumar ƙasar Kanada a Nijeriya ta yi tsokaci game da rahotonnin da ke yawo na cewa ta hana bada bisa ga jagororin tsaron Nijeriya ciki har da Janar Christopher Musa, Babban Hafsan Tsaron Nijeriya. A wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma'a, hukumar ta ce tana sane da lamarin, saidai ba za ta yi bayanin dalilin hakan ba kasancewar abu ne na sirri. Rahotonni sun bayyana cewa an gayyaci jagororin tsaron ne don karrama wasu daga cikin tsofaffin sojojin da suka halarci yaƙe-yaƙe. A yayin da wasu daga cikin tawagar suka samu bisa, wasu…
Read More

Babban jami’in Binance ya faɗi sunayen ƴan majalisar da suka nemi karɓar cin hancin Dala miliyan 150 a wajensa

Daga BELLO A. BABAJI Shugaban kamfanin yaƙi da laifukan kuɗaɗen 'crypto' na Binance, Tigran Gambaryan ya bayyana sunayen ƴan majalisar da suka nemi ya ba su cin-hancin Dala miliyan 150. A watan Oktoban shekarar 2024 ne aka sako Gambaryan bayan watanni, sakamakon janye tuhumar badaƙalar kuɗaɗe da Gwamnatin Tarayya ta shigar akan kamfaninsa, wanda hakan ya biyo bayan shiga tsakani da Gwamnatin Amurka ta yi. A lokacin da aka tsare shi, Gambaryan ya ce akwai wasu ƴan majalisa da suka buƙaci ya ba su cin-hanci don ya kuɓuta daga kamawa ko maka shi a kotu. A wani rubutu da ya…
Read More

Duk da bada haƙuri, MTN ta ƙara kuɗin kira

Daga BELLO A. BABAJI Kamfanin MTN ya ƙara farashin kira zuwa N13.8 a kowane minti daga N7.8. Wani bincike ya nuna cewa an yi wani kira na daƙiƙu 62 aka, lamarin da ya nuna an samun ƙarin farashi da kaso 43. Hakan ya biyo bayan haƙuri da kamfanin ya bayar na ƙara kashi 200 ne ga kuɗin datar giga 15. A wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Instagram a ranar Alhamis, MTN ya ce an samu kuskure a lissafin gyaran farashin, inda ya tabbatar wa kwastomomi cewa yana ƙoƙarin ganin an samu sabis mai kyau a nan gaba.
Read More

Jami’ar UNIZIK ta kori ɗalibar da ta casa lakcara

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar gudanarwa ta Jami'ar Nnamdi Azikwe, ta tabbatar da korar wata ɗaliba mai suna Goddy-Mbakwe Chimamaka Prescious, bayan samun ta da laifin lakaɗa wa malami duka akan bidiyon TikTok a jami'ar. Rajistiran riƙon ƙwarya na jami'ar, Victor Modebelu ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Juma'a. Ya ce Shugaban jami'ar ya samu rahoto daga kwamitin hukunta ɗalibai akan dukan da ta yi wa wani lakcara daga tsangayar nazarin wasan kwaikwayo. Sanarwar ta ce an kama Chimamaka ne da laifin rashin ladabi da ƙarya dokokin kundin dokar zama ɗalibi, wanda a saboda haka…
Read More

Za a yi alfahari da Hukumar NEDC bisa zuba jari a ilimi da fasaha – Shettima

Daga BELLO A. BABAJI Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya ce nan gaba za a yi alfahari da Hukumar Ci-gaban Shiyyar Arewa-maso-Gabas (NEDC) saboda ƙoƙarinta na faɗaɗa hanyoyin samun ababan ci-gaba na more rayuwa, wadda ta zuba jari a harkar ilimi da fasahar 'green technology' ta shirin 'Accelerated Senior Secondary School', wato ASSEP. Ya bayyana shirin ASSEP a matsayin wani salo na dacewa da tafiyar zamani, ya na mai cewa ilimi shi ne abinda zai sa yaro ya zama abin alfahari acikin al'umma. Shettima ya faɗi haka ne a ranar Alhamis, a yayin wani zama da tawagar gudanarwar NEDC a…
Read More

Mutane da dama sun rasu bayan tirela ta ƙwace a Kano

Daga BELLO A. BABAJI Mutane da dama sun rasa rayukansu a yayin da wata tirela ta ƙwace a gadar Muhammadu Buhari dake Jihar Kano. Haka kuma wasu sun samu raunuka a yayin da iftila'in ya auku da motar, wadda ta nufi Kudancin Nijeriya a yau Juma'a. Kamar yadda wani mai amfani da shafin Facebook mai suna Yahaya Abubakar Sadiq ya wallafa, ya ce lamarin ya faru ne daga Mariri a Hotoro zuwa Unguwa Uku inda tirelar ta kife ɗauke da mutane sama da 20 da wasu kayayyaki. Wani shaida mai suna Shu'aibu Hamisu ya ce motar ta ƙwace ne daga…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Shahararren jagoran ƙungiyar Afenifere, Ayo Adebanjo ya rasu

Daga BELLO A. BABAJI Sanannen jagoran ƙungiyar kabilar Yoruba ta Afenifere, Pa Ayo Adebanjo ya rasu bayan shafe shekaru 96 a duniya. Iyalansa suka bayyana hakan a wata takarda da suka aika wa manema labarai a ranar Juma'a, 14 ga watan Fabrairu, Takardar, wadda ke ɗauke da sanya hannun wasu daga cikin iyalan nasa da suka haɗa da Misis Ayotunde Atteh (nee Ayo-Adebanjo), Misis Adeola Azeez (nee Ayo-Adebanjo), da kuma Mista Obafemi Ayo-Adebanjo ta ce marigayin ya rasu ne a gidansa dake Lekki a Jihar Legas. Adebanjo tsohon lauya ne kuma Sakataren shirye-shirye na jam'iyyar Action Group, sannan kuma ɗaya…
Read More

Saudiyya ta haramta shan barasa a Gasar Kofin Duniya na 2034

Daga BELLO A. BABAJI Jakadan Saudiyya ga Birtaniya ya ce ba za a amince da shan giya a lokacin gasar kofin duniya na shekarar 2034 da ƙasar za ta jagoranta ba. A wata hira da LBC ta yi da shi, Khalid bin Badar Al Saud ya ce ba za a sayar da barasa a ko'ina a ƙasar ba a yayin gudanar da gasar ciki har da otal-otal. Ya kuma ce za a iya samun nishaɗi ta hanyoyi da dama, ya na mai cewa haka al'adarsu ta ke, don haka ba za su canza ta ba saboda buƙatar wasu. Hakan na…
Read More

MOPPAN ta haɗa kai da NFVCB don bunƙasa Kannywood

Daga BELLO A. BABAJI A ƙoƙarinsu na faɗaɗa matakan haɗa kai da wasu ɓangarori don bunƙasa harkokin masana'antar finafinai ta Kannywood, Shugaban ƙungiyar ƴan fim ta ƙasa (MOPPAN), Mal. Mai-Kuɗi Umar da mataimakinsa na Arewa maso Yamma, Alhaji Bala Kufena, sun gana da Babban Daraktan Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa (NFVCB), Dakta Shaibu Hussaini a ofishinsa dake Abuja. Jagororin na MOPPAN sun miƙa takardar neman agajin kayayyakin aiki da taron ƙara wa juna sani na haɗaka da wasu nau'ukan tattauna muhimman batutuwa da za su amfanar da Kannywood. Wannan wani mataki ne da MOPPAN ta ɗauka don inganta harkokin masana'antar…
Read More

‘Yar Nijeriyar da ta rasa mafaka a Birtaniya sau takwas, ta yi nasara bayan shiga IPOB

Daga BELLO A. BABAJI Daga ƙarshe, wata ƴar Nijeriya da ta rasa damar zama a ƙasar Birtaniya har sau takwas, ta yi nasarar samu bayan da ta amince ta shiga ƙungiyar masu fafutukar kafa yankin ƴan Biafra, wato IPOB. Wani alƙali yi a ce matar mai mai shekaru 49, wadda ba a bayyana sunanta ba, ta samu nasarar ne biyo bayan amincewa ta zama mambar IPOB. A shekarar 2011 ne matar ta koma Britaniya inda kuma ta shiga IPOB a 2017. Kamar yadda aka sani, Gwamnatin Nijeriya ta ayyana IPOB a matsayin ƙungiyar ta'addanci, yayin da a Tarayyar Turai kuwa…
Read More