13
Feb
Daga BELLO A. BABAJI Kwamishinan Labarai da Harkokin Cikin gida na Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya jaddada aniyar gwamnatin jihar ta bunƙasa harkar ƙirƙira ta digital da inganta matasa ta fasahar Artificial intelligence, wato AI. A lokacin da ya kai ziyara a ofishin Afrilab na AI a Zaria, Kwamishinan ya sanya ido kan ayyuka da kayayyakin horo na kamfanin, ya ce abubuwa ne da za su taimaka wa matasa masu tasowa wajen ƙwarewa a ɓangarori daban-daban na AI. Ya ce ziyarar ta biyo bayan umarnin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar, domin tattauna yiwuwar mayar da ayyukan Afrilab…
