12
Feb
Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada aniyarta ta cigaba da kula da yara da inganta rayukansu ta hanyar samar da shirye-shirye da za su bada damar samun ilimi da kiwon lafiya da walwalarsu acikin al'umma. A wata sanarwa da Daraktan Ayyuka na musamman, Sani Abba Yola na Ma'aikatar Labarai da Harkokin Cikin gida ya fitar, Kwamishina, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya bayyana hakan ne a yayin taron inganta al'umma da aka yi wa ɗalibai a Jami'ar Bayero da ma'aikatar ta shirya da haɗin-gwiwar Asusun Kula da yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, wato UNICEF. Ya ce a ƙoƙarinsu…
