Babaji

5706 Posts

Hamas ta sako fursunonin Isra’ila uku a musayar Palastinawa 183

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Asabar ne mayaƙan Hamas ta sako ƙarin wasu fursunonin Isra'ila guda uku akan musayar Palastinawa 183 da Isra'ila ta sako a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza. An gudanar da wakoki gabannin musayar a birnin Deir Al-Balah a safiyar Asabar da jami'an bada agaji na Red Cross da wasu ƴan Hamas suka jagoranta. Jami'an Red Cross ne suka gabatar da fursunoni ukun ga sojojin Isra'ila a yankin Kudancin ƙasar inda suke karɓar kulawar lafiya a matakin farko. Wata sanarwa da hukumomin tsaro na Isra'ila suka fitar, ta ce sun yi kira…
Read More

Saudiyya ta dakatar da bizar shiga ƙasarta da yawa ga Nijeriya da ƙasashe 13

Daga BELLO A. BABAJI Ƙasar Saudiyya ta fitar da sabon tsarin biza da zai shafi matafiya daga Nijeriya da wasu ƙasashe 13, wanda zai taƙaice masu zirga-zirgar shiga zuwa sau ɗaya a wata guda ba tare da zaɓin ƙari ba. Hukumomi sun bayyana cewa bizar da ke bada damar shiga sau wani adadi a kan yi amfani da ita ta hanyoyin da ba su dace inda wasu ke amfani da ita wajen zama na tsawon lokaci da kuma yin aikin hajji ba a hukumance ba. Hakan na zuwa ne bayan samun mahajjata 1,200 da suka rasa rayukansu a hajjin shekarar…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Nnamdi Kanu ya sake zuwa kotu da neman Alƙali Nyako ta tsame hannunta a shari’arsa

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Litinin ne aka samu wani wasan kwaikwayo a Babbar Kotun Tarayya dake Abuja, inda lauyan Nnamdi Kanu, Aloy Ejimakor ya faɗa wa Mai Shari'a Binta Nyako cewa ta tsame hannunta a shari'ar wanda ya ke karewa. Saidai Mai Shari'ar ta mayar da martani da cewa Babban Alƙali bai amince da ta cire hannu a shari'ar ba, wanda ya sake mayar mata da ƙarar a ƙarƙashin ikonta. Ta faɗa wa tawagar masu kare wanda aka shigar ƙarar ƙarƙarshin jagorancin Ejimakor cewa su aiko a rubuce matuƙar suka nace akan sai ta cire hannu a shari'ar.…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Fubara ya janye ƙalubalantar Kakaki Amaewhule kan Majalisar Dokokin Ribas a Kotun Ƙoli

Daga BELLO A. BABAJI Kotun Ƙoli a Abuja, ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar da Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara ya yi game da ƙalubalantar shuagabancin Majalisar Dokokin jihar. Ta kuma umarci Fubara da ya biya tarar Naira miliyan biyu ga majalisar da Amaewhule ga kwamitin mutane biyar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Uwani Abba-Aji a ranar Litinin. Hakan na zuwa ne a lokacin da lauyan gwamnan, Yusuf Ali, ya janye ƙarar. Sauran bayanai za su zo daga baya…
Read More

An kama fasto yana kai wa ƴan ta’adda bindiga a Filato da Kaduna

Daga BELLO A. BABAJI Rundunar ƴan sanda ta yi nasarar kama wani fasto da wasu da ake zarginsu da hannu a kai wa ƴan ta'adda bindigu a Jihohin Kaduna da Filato da wasu yankunan Jihar Nasarawa. Kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi ya bayyana hakan a lokacin da aka gurfanar da waɗanda ake zargin a makon da ya gabata a Abuja. Ya ce jami'an sirri na IRT a Filato sun kama mutanen ne a wurare mabanbanta waɗanda mambobi ne na tawagar safarar haramtattun bindigu. A yayin atisayensu ne suka gano wani rumbun makamai da ceto wasu mutane da aka yi garkuwa da…
Read More

Gobarar tankar gas ta yi sanadin ƙone motoci da shaguna a Neja

Daga BELLO A. BABAJI An sake samun wani hatsarin gobara a Jihar Neja bayan da wani abin fashewa ya tarwatse a yankin Sabon-Wuse na ƙaramar hukumar Tafa, wanda ya yi sanadiyyar ƙone wasu motoci da shaguna. Darakta-Janar na Hukumar Bada Agajin Gaggawa a jihar (NSEMA), Abdullahi Baba-Arah ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Lahadi inda ya ce ba a samu asarar rayuka ba. Lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 11 na dare a ranar Asabar, a lokacin da wata tanka ta ke sauke gas a wani gidan mai. Shaidu sun bayyana cewa al'amarin ya sanya al'umma cikin fargaba…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: An yi waje da Liverpool a kofin FA

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar da ke jagorantar teburin Frimiyar ƙasar Ingila, wato Liverpool, ta yi rashin nasara da ci ɗaya da nema a hannun Plymouth a wasan kofin FA, wanda hakan ya nuna an yi waje da ita a gasar na wannan kakar. Hakan ya rushe tsammaninta na lashe kofuna huɗu da ta ke ciki inda a makon da ya gabata ne ta kai wasan ƙarshe a gasar Carabo. Yanzu haka dai Liverpool ita ce ta ɗaya a Frimiya lig da ratar maki shida da kuma kwanten wasa ɗaya. A minti na 53 ne ɗan wasan Plymouth, Ryan Hardie…
Read More

Gwamna AA Sule ya koka da sayar da guraben aiki ga malamai 2,277 a Nasarawa

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana yadda jami'an gwamnati suka sayar da guraben aiki ga masu neman aikin koyarwa guda 2,277 a jihar. Ya kuma yi barazanar miƙa al'amarin ga jami'an Hukumar Kula da Malamai ta jihar (NSTSC) da aka dakatar daga aiki ga hukumomin tsaro, bisa zargin su da karɓar kuɗaɗe daga hannun waɗanda ke neman aikin karantarwa. Lamarin ya biyo bayan karɓar rahoton kwamitin bincike game da badaƙalar da aka yi na ɗaukar malamai a NSTSC ne da AA Sule ya yi a Fadar Gwamnatin jihar. Ya bayyana hakan a matsayin abinda ya saɓa…
Read More

Gwamnan Kano ya naɗa Umar Farouk a matsayin sabon sakataren gwamnati

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya naɗa Umar Farouk Ibrahim a matsayin sabon sakataren gwamnatin jihar (SSG). Kakakinsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya faɗi hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Asabar inda ya ce naɗin zai fara aiki ne daga ranar Litinin, 10 ga watan Fabrairu. Ya ce an naɗa Ibrahim ne sakamakon gogewa da ƙwarewarsa ta fuskar jagoranci wanda ake fatan hakan zai taimaka wajen haɓaka ayyukan ci-gaba a jihar. Sabon SSGn ya kasance ma'aikacin gwamnati daga shekarar 1987 zuwa 2023 inda ya riƙe muƙamai a mataki daban-daban wanda hakan ya taimaka…
Read More

Mun kashe mataimakan Bello Turji – Babban Hafsan Tsaron Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa ya ce dakarunsu sun yi nasarar hallaka manyan kwamandojin sansanin jagoran ƴan bindiga, Bello Turji. Janar Musa ya bayyana hakan ne a yayin taron bikin hafsoshin tsaro na haɗaka a Abuja, ranar Juma'a. Ya ce wasu daga cikin kwamandojin da aka kashe yayin wani atisaye a ranar Alhamis, sun haɗa da Kachalla Gwammade da Kachalla Shehu. Nasarorin da sojoji suke samu akan ƴan bindiga a Zamfara sun sanya Turji shiga halin rikicewa tare da guje wa kamun dakarun a ƙoƙarinsa na tserewa, kamar yadda CDS ɗin ya bayyana.…
Read More