07
Feb
Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Wani bincike da Blueprint Manhaja ta gudanar ya nuna cewa, babu ƙamshin gaskiya a rahoton da aka wallafa da ke nuna cewa, jami’an Hukumar EFCC sun yi dirar mikiya a Hukumar Kula Da Aikin Hajji ta Nijeriya (NAHCON) suka yi awon gaban da Kakakin Hukumar, Hajiya Fatima Usara, ba gaskiya ba ne. Binciken ya nuna cewa, tun asali EFCC ta nemi wasu bayanai ne na wasu shekaru da suka gabata game da hukumar a ƙarƙashin ofishin tsohon kakakin NAHCON, wanda kuma odishin kakakin ta yanzu ta miƙa wa EFCC ɗin, kamar yadda ta buƙata.…
