Babaji

5707 Posts

An fara zuwa Nijeriya neman lafiya daga Amurka, inji Shettima

Daga BELLO A. BABAJI Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya gano cewa Nijeriya tana samun ci-gaba ta fuskar kiwon lafiya ganin yadda marasa lafiya daga Amurka da wasu ƙasashe suke zuwa don a musu dashen ƙoda cikin inganci kuma a farashi mai rahusa. Ya ce Nijeriya ta zaɓi samar da sauƙin farashi ne a jinya tare da yin sa cikin inganci la'akari da al'ummarta. Shettima ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyara da Ƙungiyar Likitocin Cutar ƙoda ta Nijeriya (NAN) ta kai masa a Fadar shugaban ƙasa dake Abuja. Ya bayyana buƙatar zuba hannun-jari a ilimin harkokin likitanci na…
Read More

Sanin Jaji ya jajenta wa waɗanda gobarar Ƙauran-Namoda ta shafa da tallafa musu

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Ƙauran-Namoda/Birnin Magaji, Hon. Aminu Sani Jaji, ya bayyana mutuwar almajirai 17 a iftila'in gobarar Ƙauran-Namoda a matsayin babban rashi ga jiharz Zamfara da ƙasa baki dyaya. Hon. Jaji a wata sanarwa da ya fitar a Gusau, ya bayyana kaɗuwarsa bisa gobarar, wadda ta lalata Makarantar Malam Ghali da ke ƙaramar hukumar Ƙauran-Namoda a jihar Zamfara, tare da yin sanadin mutuwar daliban 17 tare da jikkata wasu da dama. Jaji, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Kula da Muhalli na majalisa, ya jajenta wa Shugaban Bola Ahmed Tinubu, Gwamnati da al’ummar…
Read More

Hukumar NSCDC a Zamfara ta jajenta wa waɗanda gobarar Ƙauran-Namoda ta shafa

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Hukumar tsaro ta Civil Defense (NSCDC) reshen jihar Zamfara ta jajenta wa iyalan waɗanda gobarar makarantar allo ta shafa a ƙaramar hukumar Ƙauran-Namoda da ta yi sanadin mutuwar almajirai 17. Tawagar, ƙarƙashin jagorancin kwamandan jihar, CC Sani Mustapha sun kai ziyarar jaje ga Mai Martaba Sarkin Ƙauran-Namoda, Alh. Sanusi Muhammad Ahmad Asha, Shugaban Karamar Hukumar, Alh. Munnir Mu'azu Haidara da waɗanda lamarin ya rutsa da su. A ranar Larabar da ta gabata ne wata gobara ta laƙume rayukan dalibai almajirai 17 yayin da aka ceto wasu goma 17 da suka samu munanan raunuka. Rahotanni sun…
Read More

Yara 17 ne suka rasu a iftila’in gobarar Zamfara

Daga BELLO A BABAJI Kimanin almajirai 17 ne suka rasa rayukansu da wasu 16 da suka samu raunuka a yayin da gobara ta kama a wata makarantar Islamiyya dake ƙaramar hukumar Ƙauran-Namoda a Jihar Zamfara. Gobarar ta fara ci ne daga wani gida da ke kusa da makarantar inda ta yaɗu zuwa masaukin yaran. Tuni aka garzaya da waɗanda suka samu raunuka zuwa asibiti don ba su kulawa. Wani shaida mai suna Yahaya Mahi ya shaida wa manema labarai cewa da farko wutar ta kama ne a wani sashi na ginin da almajiran suke, wadda daga bisani ta bazu har…
Read More

Nijeriya za ta yi amfani da bashi wajen ciyar da tattalin arziƙinta gaba – Shettima

Daga BELLO A. BABAJI Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya ƙaddamar da Ofishin Masu kula da Harkokin Sarrafa Basussuka (DMO) a ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na inganta harkoki da tsare-tsaren kuɗaɗe, wanda wani ɓangare ne na Ajendar Sabonta ƙasa ta Shugaba Bola Tinubu. A lokacin da ya ke magana yayin zaman tawagar ofishin a Fadar Shugaban ƙasa a ranar Laraba, Shettima, wanda shi ne shugabanta, ya yi kira ga mambobi da su samar da salo na musamman wajen sarrafa kuɗaɗen bashi na al'umma. Ya ce Nijeriya za ta cigaba da amfani da kuɗaɗen bashi a matsayin wani ginshiƙi na haɓaka tattalin…
Read More

Gwamna Lawal Dare ya yi jimamin rasuwar almajirai 17 a gobarar da ta auku a Zamfara

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal Dare ya aika saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan almajirai 17 da suka rasa rayukansu a yayin gobarar da ta afka musu a wata makarantar allo a jihar. A wata sanarwa daga Kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris, Lawal Dare ya bayyana hakan a matsayin abin alhini da kuma tausaya wa ga waɗanda iftila'in gobarar ta shafa. A ranar Talata ne lamarin ya faru a makarantar allo ta Mallam Ghali dake ƙaramar hukumar Ƙauran-Namoda. Ya ce, a madadin Gwamnatin jihar, suna miƙa ta'aziyarsu ga iyalan mamatan da makarantar da kuma ƙasa baki ɗaya bisa rasuwar…
Read More

Ko fentin gidana ban canza ba a tsawon shekaru takwas na mulkina, inji Buhari

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa a tsawon mulkin da ya yi shekara takwas, ko sake fentin gida bai yi ba . Buhari ya faɗi haka ne a lokacin da ƙungiyar ƴan jarida reshen kafofin yaɗa labarai a Katsina suka kai masa ziyara a gidansa dake garin Daura. Ya ce yana cikin ƙoshin lafiya idan aka kwatanta shi da abokansa da suka taso tun suna yara, inda wasu daga cikinsu da sanda suke dogarawa su yi tafiya. Ya kuma ce Mataimakin Shugaban ƙasa, kashin Shattima ne ya fidda kuɗi daga aljihunsa ya ke…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Majalisar Dattawa ta tabbatar da sallamar kwamishinonin zaɓe na jihohi uku

Daga BELLO A. BABAJI Majalisar Dattawan Nijeriya ta tabbatar da tsige wasu kwamishinonin zaɓe guda uku bisa laifin bijirewa dokokin kundin dokar Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC. Tun a shekarar 2023 ne aka dakatar da manyan jami'an zaɓen, biyo bayan neman buƙatar soke naɗinsu da Shugaba Bola Tinubu ya yi, inda ya nemi majalisar da ta tabbatar da hakan. Kwamishinonin sune na jihohin Adamawa, Sokoto da Abia. Cikakken bayani zai zo daga baya….
Read More

Taron NNPP: Kwankwaso ya rasa jagorancin jam’iyyar bayan an zaɓi Agbo Major

Daga BELLO A. BABAJI An zaɓi Agbo Major a matsayin sabon shugaban jam'iyyar NNPP a yayin taron jam'iyyar na ƙasa a Otal ɗin RockView dake Apapa a jihar Legas. Taron ya samu halartar daliget da dama da mambobin jam'iyyar daga sassan Nijeriya. Sauran waɗanda aka zaɓa sun haɗa da; Oginni Olaposi a matsayin sakatare na ƙasa; Felix Chukwurah a matsayin mataimakin shugaban jam'iyya (na Kudu); Adetoyese Omokanye a matsayin ma'aji; mataimakin shugaban jam'iyya na Arewa, Bayo Muhammed da Abdulrasaq Abdulsallam a matsayin sakataren yaɗa labarai. Sai Aisha Kade a matsayin jagorar mata (woman leader), Edward Ofomona a matsayin shugaban matasa…
Read More

Ohinoyi: Gwamnatin Kogi ta ɗauki mataki bisa hukuncin kotu

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Jihar Kogi ta shigar da takardar ɗaukaka ƙara a Kotun Ɗaukaka ƙara dake Abuja bisa hukuncin Babbar Kotun Tarayya na tsige Ohinoyi na Masarautar Ibira, Tijani Ahmed Anaje. A ranar Talata ne Antoni-Janar kuma Kwamishinan Shari'a na jihar, Muzi Abdullahi, wanda shi ne na biyu cikin masu ɗaukaka ƙarar, ya bayyana hakan a Lokoja. Ya ƙalubalanci hukuncin ƙarar da Daudu Adeku-Ojiah, Hussaini Yusuf da Abdulrahmaam Suberu suka shigar wanda ke ƙalubalantar naɗin Ahmed Anaje da tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello ya yi. Mutane ukun da shigar da ƙarar sun nemi kotun da ta ayyana naɗin…
Read More