Babaji

5707 Posts

NAHCON ta ƙara wa’adin rajista ga mahajjatan 2025

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON) ta sanar da ƙara wa'adin yin rajista ga mahajjatan shekarar 2025. Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya bayyana hakan a ranar Talata, ta ofishin Kodinetan tawagar yaɗa labaran hajji na Ƙasa, Ibrahim Abubakar Nagarta. Shugaban hukumar ya ce an ƙara kwanaki 10 na yin rajistar ne domin bai wa wasu maniyyata damar shiga sahun masu zuwa aikin hajji a wannan shekarar. Hakan na zuwa ne kwana biyu da wa'adin rajistar ya ƙare, a ranar 2 ga watan Fabrairu. Farfesan ya kuma yi kira ga maniyyatan da su yi amfani da…
Read More

Matar Shugaba Tinubu ta ziyarci IBB da Abdulsalami a Minna

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Talata ne matar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Oluremi ta ziyarci tsofaffin shugabannin mulkin soja a Nijeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida da Janar Abdulsalami Abubakar a gidajensu dake Minna, Babban Birnin Jihar Neja. Gwamnan jihar Umaru Mohammed Bago da matarsa Fatima Bago suka marabce ta a filin jiragen sama na Bola Ahmed Tinubu dake birnin da misalin ƙarfe 10:30 na safe. Da fari dai Remi Tinubu ta je gidan IBB ne inda suka yi wata ganawar sirri ta tsawon mintina 35. Matar Mataimakin Shugaban ƙasa, Hajia Nana Shettima ita ce wadda ta mara mata baya…
Read More

Mutane da dama sun rasa rayukansu yayin fashewar tankokin fetur biyu a Adamawa

Daga BELLO A. BABAJI A jiya Talata ne wasu tankokin man fetur guda biyu suka kama da wuta a gidan MRS dake kan hanyar Numan kusa da Filin jiragen sama na Yola, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Lamarin da ya haifar da cinkoson ababen hawa a hanyar zuwa Yola, Babban Birnin jihar. Tuni dai jama'a da dama suka garzaya wajen da abin ya faru don gani da ido ba tare da la'akari da haɗarin da ke tattare da zuwa wajen ba a yayin da tankokin suke ci da wuta. Haka kuma jami'an kashe gobara daga Hukumar…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Hukumar Alhazan Sokoto ta nemi NAHCON ta ƙara wa’adin rajista ga mahajjatan 2025

Daga BELLO A. BABAJI A yayin da ake cigaba da shirye-shiryen zuwa aikin hajjin shekarar 2025, maniyyata 1,700 ne daga jihar Sokoto suka biya kuɗi a karon farko. Hukumar Jigilar Alhazan jihar ta samu masauki da shirya bada kula ga mahajjatan a ƙasa mai tsarki. Kawo yanzu kimanin Naira biliyan 5 ne jihar ta aika wa Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON). A wata sanarwa da Babban jami'in yaɗa labaran hukumar, Faruku Umar ya fitar, Sakataren hukumar, Ladan Ibrahim ya koka kan yadda da dama daga maniyyata musamma mazauna kauyuka ba su kammala biyan kuɗaɗensu ba. Ya yi kira ga NAHCON…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta ware N252b don kammala aikin titin Abuja-Kaduna-Kano

Daga BELLO A. BABAJI Gwamatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince ta ware kuɗaɗen ne a yayin zaman Majalisar Zartarwa a jiya Litinin 3 ga watan Fabrairu, a Fadar Shugaban ƙasa. Haka kuma, FEC ta amince da kasa aikin hanyar zuwa matakai biyu don samar da ingantaccen aiki akan lokaci. A yayin ganawa da manema labarai bayan kammala taron, Ministan ayyuka, David Umahi ya bayyana cewa sashe na farko zai tashi daga kan iyakar Babban Birnin Tarayya Abuja zuwa Jihar Neja, wanda aka ƙara wa kilomita 5.71 kan ainihin taswirar aikin na farko, inda sashe na biyu ya samu ƙarin…
Read More

Kwalejin Koyon Yaƙi ta Nijeriya ta karrama manyan jami’ai uku

Daga BELLO A. BABAJI Kwamandan Kwalejin Koyon Yaƙi ta Sojoji (AWCN), Manjo-Janar Umar Mohammed Alƙali, ya karrama wasu manyan jami'an makarantar da kyautar 'Distinguished Fellow Award' kan ƙoƙarinsu ga ilimin sojoji da samar da ci-gaba a jagoranci na gari. A ranar 3 ga watan Fabrairu ne aka gudanar da bikin bada lambar girmamawar ga jami'an masu muƙamin Birgediya Janar, waɗanda suka haɗa da AM Dikko (Daraktan Yaƙi da Tsare-tsare) da AU Abdul (Daraktan Shirye-shirye) da kuma NE Okoloagu (Daraktan Nazarin Sojoji da Alaƙar hukumomi). Hakan ya samu ne bayan nuna sadaukarwa da jami'an suka yi a bakin ayyukansu, wadda ta…
Read More

Gwamna Abba ya yi wa iyalan Sanata Isah Kachako ta’aziyyar rasuwarsa

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya jagoranci wasu manyan jami'an gwamnati zuwa gidan iyalan marigayi Sanata Isah Kachako, wanda ya rasu kwanaki uku da suka gabata bayan fama da wani dogon rashin lafiya. Cikin wata takarda da Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, a ranar Talata, Gwamna Abba ya bayyana mutuwar Sanatan a matsayin babban rashi ga al'ummar Kano da ma ƙasa baki ɗaya sakamakon gudunmawarsa ga ci-gaban ƙasa. Ya ce mutum ne wanda ya kasance mai sadaukarwa a matsayinsa na tsohon malamin makaranta, jami'in soja, kuma gogaggen ɗan siyasa, wanda ya tsaya…
Read More

Ka daina tozarta Kaduna – El-Rufa’i ga Uba Sani

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i ya tabbatar da ɓarakar da ke tsakanin sa da magajinsa, Gwamna Uba Sani, ya na mai alaƙanta shirin tura kuɗi (conditional cash transfer) na Shugaba Bola Tinubu a matsayin abin da ya shiga tsakaninsu. Hakan na zuwa ne a lokacin da Gwamna Uba Sani ya musanta duk wani rikici da ke tsakaninsu a yayin wata hira ta gidan telebijin na TVC a ranar Litinin, inda ya haƙiƙance akan cewa alaƙarsu tana nan yadda take a baya. Gwamnan ya kuma yi tsokaci ga ƴan siyasar da ke ƙoƙarin yin nasara…
Read More

Gwamnan Kano ya ƙaddamar da hukumomin Shari’a da Zakka a jihar

Daga BELLO A. BABAJI Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano yi ƙaddamar da shugabanni da kwamishinoni da mambobin hukumomin Shari'a da Zakka. A wata sanarwa da Kakakinsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Litinin, gwamnan ya bayyana yadda Kano ta kasance cibiyar addinin Musulunci ganin yadda ta ke da sanannun malamai, makarantun islamiyya da cibiyoyin nazarin addinin Musulunci. Ya ce an naɗa waɗanda aka bai wa muƙaman ne bisa cancanta inda hakan zai taimaka wajen sauke nauye-nauyensu bisa gaskiya da adalci. Gwamnan ya yi kira ga Hukumar Shari'a da ta tabbatar da haɗin kan al'ummar musulmi daga…
Read More

Yadda ƴan bindiga suka biya N1.5m ga sarki a Taraba don kafa sansani – Sojoji

Daga BELLO A. BABAJI Rundunar sojojin Nigeriya ta ce ƴan bindiga sun bai wa wani sarkin gargajiya Naira miliyan 1.5 don sayen filin da za su kafa sansani a yankin Amar na Jihar Taraba. Mataimakin Daraktan yaɗa labarai na riƙon ƙwarya a rundunar, Kyaftin Olubodunde Oni ya faɗi hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, inda ya ce sojoji sun tarwatsa wani sansanin ƴan bindiga a jihar tare da kashe ɗaya daga cikinsu da kuma ƙwato wani rumbun muggan makamai. Ya ce lamarin ya auku ne a yankin Angwan Bala na Kambari Janar dake Ƙaramar Hukumar Karim…
Read More