23
Sep
Daga BELLO A. BABAJI Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki ya yi kira ga al'umma su kwantar da hankali tare da ƙaurace wa tashin-tashina da lalata dukiyoyin al'umma. Obaseki ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da manema labarai bayan hukumar zaɓe, INEC ta sanar da Monday Okpebholo na jami'yyar APC a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen gwamnan jihar. A ranar Lahadi ne INEC ta sanar da nasarar ɗan takarar APC'n duk da cewa akwai zargin maguɗi a zaɓen. Ɗan takarar ɓangaren gwamnan Asue Ighodalo shi ya zo na biyu inda Obaseki ya ce an yi zaɓen tare…
