26
Jul
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Kwanaki kaɗan bayan da shugaban matatar mai ta Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote ya yi zargin cewa akwai jami'an kamfanin man fetur na ƙasa, NNPC da ke da ɓoyayyun masana'antun mai a ƙasar Malta, alƙaluma sun bayyana cewa Nijeriya ta sayo man fetur na tsabar kuɗi da adadinsa ya kai Dala biliyan 2.25 daga ƙasar. Wata sanarwa daga 'Trade Map', ta ce a shekarar 2023, Nijeriya ta shigo da man fetur na Dala biliyan 2.8 wanda hakan ya haura da kashi 342 a kan na Dala miliyan 47.5 da aka sayo a shekarar 2013. An gano cewa,…
