26
Jul
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Sufeta Janar na 'Yan sanda, Kayode Egbetokun ya Umarci duk wata tawaga da ke shirin yin zanga-zangar tsadar rayuwa a Nijeriya su bayar da bayanan da ake buƙata ga kwamishinan Ƴan sandan jihar da za a gudanar da ita. Kayode ya faɗi hakan ne a ranar Juma'a a Abuja inda ya yi kira ga al'umma da su kasance masu lura da hangen nesa kafin shiga kowace irin zanga-zanga dan gujewa haifar da koma baya wa ƙasa. Abubuwan da ake buƙatar bayaninsu daga kowace tawaga ta zanga-zangar sun haɗa da; * hanyoyin da za a bi da…
