Babaji

5435 Posts

An dakatar da Cynthia ta Nijeriya daga gasar Olympics bisa gwajin ƙwayoyi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI An dakatar da ƴar wasan 'boxing' ta Nijeriya, Cynthia Ogunsemilore daga shiga gasar Olympics sakamakon gwajin ƙwayoyi da aka yi mata a ranar Asabar a yayin da ake cigaba da shirin wasanta na farko. Hukumar gwajin ƙwayoyi ta ƙasa-da-ƙasa, ta ce bayan gwajin Cynthia an tabbatar cewa ta na shan maganin 'furosemide wanda yana daga cikin ababan da hukumar ta haramta wa ƴan wasa. Shafin ATI ya wallafa cewa, a halin yanzu an dakatar da ita har sai an warwara matsalar kamar yadda ya ke a cikin dokokin kwamitin gasar. Sannan, hakan ya nuna cewa Cynthia…
Read More

Gwamnati ta ƙaryata jawabin ‘Tinubu Speaks’ da ke yawo

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A wani yunƙurin gaggawa game da wani jawabi da aka yi wa laƙabi da 'Tinubu Speaks' da ake danganta shi da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata abin da ke ciki tare da nesanta Shugaban da shi. A ranar Asabar ne Mai magana da yawun Shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ya yi watsi da saƙon, yana mai cewa ba gaskiya ne abin da ake jingina wa Shugaba Tinubu. Ana yaɗa ƙirƙirarren labarin ne a kafafen sada zumunta kan cewa wani jawabi ne da Tinubu ya yi inda ya ke magana game da ƙalubalen da…
Read More

NIS ta dakatar da ɗaukar hutu ga ma’aikata kan zanga-zangar tsadar rayuwa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI La'akari da zanga-zangar tsadar rayuwa da ke tafe a watan Agusta, hukumar shige da fice, NIS ta sanar da dakatar da neman zuwa hutu ga ma'aikatanta na wucin-gadi. Kwamturola Janar ta hukumar, Misis Kemi Nandap ta bada umarni ga shugabannin shiyyoyi da na jihohi da kuma na yankuna, inda ta ce akwai buƙatar aiki na musamman a kan iyakokin ƙasa domin tabbatar da tsaro a lokacin zanga-zangar. Cikin wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na hukumar, Kenneth Udo ya fitar, hukumar ta ce tana shirye-shirye domin tsare duk wani kutse da ka iya tunkaro ƙasar…
Read More

Majalisar Wakilai ta shirya neman a tsige Kyari daga shugabancin NNPC

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Majalisar Wakilai ta yi barazanar kiran a tsige shugaban kamfanin man fetur na Ƙasa (NNPC), Mele Kyari idan ya cigaba da takurawa ayyukan matatar Ɗangote. Mataimakin kakakin majalisar, Philip Agbese ya faɗi hakan a yayin hira da manema labaru a Abuja. Haka nan, Agbese ya ce Majalisar ta bayyana goyon bayanta game da tsige shugaban hukumar tace man fetur ta Ƙasa (NMDPRA), Umar Farouk, yana mai cewa NNPCL da NMDPRA sun nuna kushewarsu da ƙiyayya ga matatar Ɗangote wanda hakan ya haifar da matsaloli wa ƙasa Nijeriya. Ya ƙara da cewa, tuni dai Majalisa ta umarci…
Read More

Ki bayyana yadda za a magance matsaloli madadin takura wa zanga-zanga, CISLAC ga Gwamnatin Tarayya

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Cibiyar tabbatar da dokoki wa al'umma, CISLAC ta yi kira ga gwamnatin Nijeriya ta tsara jadawalin magance koken ƴan ƙasa a madadin sanya takunkumi ga zanga-zanga. Daraktan CISLAC, Kwamared Auwal Musa Rafsanjani ya nuna buƙatar gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa game da matsalolin hauhawar farashi, rashin aikin yi, rashawa, rashin tsaro da kuma rarrabewar cibiyoyi. Rafsanjani ya yi kira ga gwamnati ta ɗauki matakin bada kariya ga masu zanga-zanga, yana mai cewa dokar ƙasa ta amince da zanga-zangar lumana. Haka nan, ya bukaci ƙananan hukumomi da jihohi su bi hanyoyin da suka dace wajen fuskantar matsalolin…
Read More

Ku bada ƙarfinku ga zaɓe maimakon zanga-zanga – Kwankwaso

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da laifuka shida na siyasa da tattali yayin da ya buƙaci al'ummar Nijeriya su mayar da hankali kan zaɓe ba zanga-zanga ba. Kwankwaso ya faɗi haka a ranar Asabar cikin wata sanarwa da ya fitar game da batun zanga-zangar 'EndBadGovernment', yana mai nuna damuwa kan halin da Nijeriya ta tsinci kanta inda ya danganta hakan da gazawar gwamanti tun daga shekarar 2007. Ya ce, shugabanci mai kyau da adalci na girmama dokar ƙasa, bayyanawa ga kowa,…
Read More

Ofishin jakadancin Amurka ya yi gargaɗi kan zanga-zangar gama-gari a Nijeriya

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya ya yi gargaɗi game da zanga-zangar gama-gari da ake shirin yi a Nijeriya wanda ake tsammanin farawar sa daga 29 ga watan Yuli zuwa 5 ga watan Agusta. Sanarwar ta wacce ta fito daga ofishin, ta ce zanga-zangar ka iya haifar da tare hanyoyi, madakatun bincike, cinkoson ababan hawa da artabu na gaba-da-gaba duk da cewa ba a san takamaiman wuraren da hakan za su faru ba. Domin kaucewa faɗawa cikin haɗari, ofishin jakadancin ya bada shawarwari kamar haka; Bibiyar gidajen jaridu na gida domin samun labaru da ɗumi-ɗuminsu, nisantar tarurruka,…
Read More

Lauyoyi sun ja kunnen Sufeto Janar kan kawo cikas ga zanga-zangar lumana

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Yayin da ake cigaba da shirin zanga-zanga a faɗin Nijeriya, lauyan kare ƴancin Ɗan Adam, Inibehe Effiong ya aika da saƙo ga Sufeto Janar na 'Yan sanda, Kayode Egbetokun inda ya buƙaci a bai wa masu zanga-zangar kariya. Effiong ya ce zanga-zangar lumana a dokar Nijeriya ta halatta, dan haka akwai buƙatar hukumomin tsaro su ba su kariya, ya na mai kafa hujja da sakin-layi na 39 da na 40 na kundin dokar ƙasa. Ya ƙara da kira ga Sufetan, ya umarci dukkan kwamishinoni da ɓangarorin da ke da alhakin bayar da tsaro ga al'umma domin…
Read More

Kotu ta yanke wa ƴan Boko Haram 125 hukunci

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Aƙalla mayaƙan Boko Haram 125 tare da masu ɗaukar nauyinsu ne aka yanke wa hukunci a bainar jama'a a wani zama na kwana biyu a Kainji da ke jihar Nija. An same su ne laifukan ta'addancin kan iyaka, tallafa wa ta'addanci da wasu lafukan kotun fashin ƙasa-da-ƙasa. Antoni Janar na ƙasa kuma Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi, shi ne wanda ke sanya ido kan lamarin hukuncin tare da haɗin gwiwar ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro. An gudanar da hukuncin ne a ranakun Talata da Laraba wanda masu shari'a biyar daga babbar kotun…
Read More

Zanga-zangar tsadar rayuwa: Rundunar ‘Yan sanda ta baza jami’ai 4,200 a Abuja

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Rundunar 'Yan sandan Abuja ta ɗauki matakin baza jami'ainta a lunguna da saƙo-saƙo na babban birnin sakamakon zanga-zangar tsadar rayuwa da wasu masu ƙishin al'umma da matasa su ka shirya yi a faɗin Nijeriya. Mai magana da yawun rundunar, SP Josephine Edeh ta bayyana hakan wa manema labarai a ranar Juma'a, inda ta ce sun ɗauki matakin bada kariya wa al'umma ta hanyar yin bincike ga masu zanga-zangar a wurare daban-daban da haɗin gwiwar wasu hukumomin tsaro. Ta ce, Kwamishinan babban birnin, Benneth Igweh a lokacin da ya ke magana akan damar ƴanci da dokar ƙasa…
Read More