Babaji

5442 Posts

Zanga-zanga: NYSC ta dakatar da tantancewar alawus ga ƴan hidimar ƙasa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumar kula da yi wa Ƙasa hidima, NYSC ta dakatar da tantancewar biyan alawus da ' zaman mako-mako da ma'aikatanta da aka fi sani da ƴan bautar Ƙasa ke yi na wucin-gadi sakamakon zanga-zangar gama-gari da ake shirin gudanarwa a sassan Nijeriya. An samu sanarwar hakan ne daga ofishin hukumar inda ta ke umurtar wakilanta na jihohi, ƙananan hukumomi da yankuna da su dakatar da ayyuka. Hukumar ta haramta wa ƴan hidimar ƙasar shiga cikin zanga-zangar, tana mai ƙarawa da cewa za ta sanar da lokacin da za a cigaba da ayyukan tantancewar da sauransu. Kazalika,…
Read More

Sufeto Janar ya umarci Rundunar ‘Yan Sanda ta bai wa ƴan zanga-zanga kariya

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Sufeto Janar na 'Yan sanda, Kayode Egbetokun ya umarci manyan jami'an hukumar da su bai wa ƴan zanga-zanga kariya wacce za a fara daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta. Kayode ya faɗi hakan cikin wani saƙo da ya fitar bayan da wani babban lauyan kare ƴancin Ɗan Adam, Ebun-Olu Adegboruwa (SAN) ya nemi Sufeton ya ɗauki matakin bai wa ƴan zanga-zangar kariya. Haka nan, Kayode ya buƙaci haɗuwa da lauyan don tattauna muhimman abubuwa kan batun inda za su gana a ranar Talata, 30 ga watan Yuli. Zanga-zangar, wacce ta ɗauki hankalin al'umma musamman…
Read More

Zanga-zanga: Amurka, Birtaniya da Canada sun gargaɗi al’umma kan tsaro

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƙasashen Amurka, Birtaniya da Canada sun ankarar da al'ummar Nijeriya game yiwuwar aukuwar tashin-tashina yayin zanga-zangar tsadar rayuwa da za a fara a ranar Alhamis. Ƙasashen sun aika sakonnin ne ta mabanbanta hanyoyi inda su ka gargaɗi mutanensu da su ƙaurace wa artabu da ka iya aukuwa tsakanin jami'an tsaro da ƴan zanga-zanga, su na masu bada misali da ire-iren yadda su ka faru a baya. Sannan, saƙonnin sun iso ne bayan da manyan ƴan kasuwa a jihohin Abuja, Sakkwato, Kano, Katsina, Ogun, Osun, Zamfara, Gombe da wasu yankunan Nijeriya su ka buƙaci a tsaurara tsaro…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Majalisa ta kira taron gaggawa kan zanga-zanga

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugaban Majalisar Dattijai, Godswill Akpabio ya kira taron gaggawa na ƴan Majalisar. Sanarwar kiran ta fito daga ofishin akawonsa, Chinedu Akubueze a ranar Litinin inda ya ce za a yi taron ne musamman kan ababan da ke damun ƙasa a halin yanzu. Za a gudanar da taron ne a ranar Laraba, 31 ga watan Yuli, 2024 da misalin ƙarfe 12 na rana, kwana ɗaya kafin fara zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya. Sanarwar ta ƙara da cewa, ana buƙatar sanatoci su yi duk shirye-shiryen da su ka dace don tattauna batutuwa masu muhimmanci ga ƙasa, majalisar…
Read More

Zanga-zanga: Ku tabbatar da tsaro a makarantu, Gwamnatin Tarayya ga shugabannin jami’o’i

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Yayin da ake cigaba da kusantar kwanakin zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya, Ministan Ilimi, Tahir Mamman, ya umarci shugabannin jami'o'i su shirya matakan kariya don bai wa makarantunsu da malamai da ɗalibai tsaro a lokacin zanga-zangar. Sakataren hukumar kula da jami'o'i ta Ƙasa (NUC), Chris Maiyaki ya fitar da wata sanarwa a ranar Litinin, ya na mai umartar shugabannin jami'o'i su fitar da jawabai na tabbatar da tsaro ga malamai da ɗaliban makarantunsu. Maiyaki, ya kuma shawarci ɗalibai da su kasance a cikin makarantu tare da mayar da hankali kan karatunsu domin kauce wa haɗuran…
Read More

Sojoji sun karɓe ragamar kula da manyan titinan Abuja kwana uku kafin zanga-zanga

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI An samu matsewar ababan hawa a babbar hanyar Keffi-Abuja yayin da jami'an soji su ka datse wani yanki domin gudanar da bincike kafin shiga Birnin Tarayyar Abuja. Sojojin sun tare daidai barikin sojoji na Abacha da ke kusa da shataletalen AYA. Kasancewar hukumomin tsaro ba su bada sanarwar hakan ba, an samu cinkoson ababan hawa wanda ya kai har gadar Nyanya, kilomita 12 kafin wajen da aka datse. Da dama daga cikin ma'aikata da ƙananan ƴan kasuwa na Abuja da ke zama a Nyanya, Maraba, Karu da Masaka, an tilasta mu su komawa gida bayan tsawon…
Read More

‘Yan bindiga sun kai hari sansanin hukumar Kwastom, sun kashe jami’i da garkuwa da wani

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƴan bindiga sun kashe jami'in Kwastom tare da yin garkuwa da wani a harin da su ka kai sansanin hukumar a yankin Koko/Besse da ke Jihar Kebbi. Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar a Jihar, Tajuddeen Salisu ya ce al'amarin ya faru ne a ranar Alhamis. Ya bayyana cewa, bayan garkuwa da ɗaya jami'in, ƴan bindigar sun kuma buƙaci maƙudan kuɗaɗe domin sako shi. Ya ƙara da cewa, an karɓi gawar jami'in da aka kashe shi ta hanyar yanka tare da kai shi Jihar Kaduna domin yi masa jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar. Kazalika,…
Read More

Da ƊUMI-ƊUMI: Zanga-zangar yunwa ta ɓarke a Neja

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wasu matasa a Jihar Neja sun fito cikin gari domin zanga-zangar tsadar rayuwa da ake fama da shi a Nijeriya. Matasan sun fito da alluna da ke ɗauke da batutuwa kamar haka; 'Enough is Enough', Stop 'Anti-Masses Policies', 'We Are Not Slaves In Our Country', 'Hardship Is Unbearable', 'Fuel Subsidy Must Be Back' da sauransu. A lokacin zagayen, matasan na rera wakokin da ke nuna adawa da gwamnati. Gwamnatin Tarayya da na jihohi sun yi ta ƙoƙarin dakatar da zanga-zangar saboda kar ɓata-gari su yi amfani da shi wajen haddasa fitina a ƙasa daga waɗanda ke…
Read More

Yadda farashin man fetur ya kai N1,300 a jihohi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Sakamakon bushewa da rijiyoyin man fetur da dama su ka yi, an samu layuka a gidajen mai a jihohin Kano, Legas, Kaduna, Ribas, wasu yankuna na Abuja, Nija da wasu jihohi a faɗin Nijeriya. Rahotanni sun bayyana cewa, hakan ya sa ƴan bunburutu su ke amfani da damarsu wajen sayar da duk lita ɗaya a farashin N1,300 da N1,500 a jihohin Legas da Ogun. An fara samun yawaitar layin man ne tun ranar Asabar a jihohin inda kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPC ya ce hakan na faruwa ne sakamakon tseko da ake samu wajen ɗakko…
Read More

Ba yaudara a rarrashin da Tinubu ke yi kan zanga-zanga – Sanata Barau

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Barau I. Jibrin ya roƙi masu shirya zanga-zangar gama-gari su sake yin nazari kan hukuncinsu tare da janye wa daga batun, don kar a yamutsa sauran zaman lafiyar da ya rage wa Nijeriya. Barau, wanda shi ne Mataimankin Kakakin Majalisar ECOWAS na farko, ya ce Tinubu na muhimmin ƙoƙari wajen ganin an magance matsalolin Nijeriya. Wata takarda da ta fito daga ofishin mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ismail Mudashir, ta ce Barau ya yi kira ga masu hura wutar zanga-zangar kan cewa su bai wa Shugaba Tinubu ƙarin…
Read More