23
Jul
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Kwamishinan 'Yan sandan birnin tarayya, Abuja, Bennet Igweh ya roƙi al'ummar jihar kar su shiga zanga-zangar da aka shirya za a yi a watan Agusta kan tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya. Igweh ya nuna damuwarsa kasancewar ɓata gari ka iya amfani da zanga-zangar wajen tarwatsa sabbin ayyukan cigaba da a ka yi a faɗin jihar. Kwamishinan, ya bayyana hakan ne a yayin hira da manema labarai a ranar Litinin a lokacin da rundunar ta gurfanar da mutane da dama kan zargin fashi a hedkwatar ofisoshinta da ke birnin. Ya ce, suna aiki tuƙuru wajen kamo ƴan…
