16
Jul
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumar zaɓe ta jihar Kogi ta ayyana 19 ga watan Oktoban shekarar nan a matsayin ranar da za ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a faɗin jihar. Hukumar ta yi sanarwar ne yayin da ake ganin hakan bai rasa nasaba da hukuncin kotun ƙoli na ranar 11 ga watan Yuli kan zartar da cin gashin kai ga ƙananan hukumomi. Kotun ƙolin ta ce daga ranar da ta yi hukuncin, dukkan ƙananan hukumomi za su koma karɓar kasafinsu daga ofishin Akanta Janar na ƙasa ba tare da wani shamaki ba, sannan kuma ta bayyana rashin halascin kwamitin…
