Babaji

5435 Posts

An cinna gobara a fadar Sarki Sanusi

Daga FAROUK ABBAS Wani rahoto daga jihar Kano ya ce gobara ta kama a fadar Sarki Sanusi da ke Gidan Rumfa wanda ake zargin waɗansu da ba'a san ko su waye ba ne suka cinna ta, inda a nan ne Sarkin ya ke. Lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 11 na daren Juma'a, a Ƙofar Kudu wanda a nan ne Sarkin ya ke zaman kotu duk ranar Litinin. Wani mutum da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce suna zargin an buɗe mukullin ƙofar ne da ƙarfi sai kuma aka shiga ciki aka cinna wuta kana sai aka sake…
Read More

An shiga juyayi yayin da ruftawar ginin makaranta ya kashe mutum 22 da raunata 120

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu da wasu da dama daga cikin ƴan Nijeriya sun jajenta wa waɗanda ruftawar ginin makaranta ya rutsa da su a Jos wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka 22 da kuma raunata wasu 120. Jaridar 'Intel Region', ta ruwaito cewa lamarin ya auku ne a yayinda ɗalibai suka shige ajijuwa a safiyar ranar Juma'a a makarantar Saint Academy da ke Busa Buji a jihar Filato. Aƙalla, lamarin ya shafi ɗalibai 200 cikin na gidaje 400 na makarantar sakandaren waɗanda galibin su ƴan shekaru 15 ne ko ƙasa da haka. A lokacin da yake…
Read More

Matasa sun shirya zanga-zanga a Kenya kan shugaban ƙasar ya yi murabus

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Matasa a ƙasar Kenya sun yi watsi da hukuncin Shugaban ƙasar, William Ruto na korar da dama daga cikin manyan ma'aikatansa inda suka ce za su yi zanga-zangar neman ya yi murabus daga muƙaminsa matuƙar bai janye daga batun aiwatar da hakan ba. Shugaba Ruto ya yi ta ƙoƙarin dakatar da fitina a ƙasarsa inda a kwanakin baya ne aka shirya wani zanga-zanga na ƙin amincewa da hauhawar kuɗin haraji inda hakan ya rikiɗe zuwa tashin-tashina da ya faɗaɗa zuwa ƙiyayya ga gwamnatin. Zanga-zangar wacce aka shirya ta kafar sadarwa da wasu taron matasa ƴan 'Gen-Z…
Read More

An buƙaci gwamnan Kaduna ya cire kwamitin riƙon ƙwarya a Birnin-Gwari

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wata ƙungiya mai suna 'Birnin-Gwari Vanguard for Security and Good Governance' da ke jihar Kaduna ta yi kira ga gwamnatin jihar da sauran masu-ruwa-da-tsaki da a rushe kwamitin riƙon ƙwarya na ƙaramar hukumar Birnin-Gwari tare da ɗora zaɓaɓɓen ɗan takara. Ƙungiyar ta yi hakan ne bayan da kotun ƙoli ta yanke hukuncin cin gashin kai ga ƙananan hukumomi inda ta ce naɗa kwamitin riƙon ƙwarya da gwamnatin Kaduna ta yi a Birnin-Gwari ya ci karo da sakin layi na 7 a kundin shekarar 1999 na dokar ƙasa kamar yadda kotun ƙoli ta tabbatar. Wata takarda da…
Read More

Yadda gini ya rufta wa ɗalibai ana tsaka da jarrabawa a Filato

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Rahotanni daga jihar Filato na cewa mutane da dama ne ruftawar gini ya rutsa da su a yayinda ake tsaka da rubuta jarrabawa a wata makaranta. Lamarin ya auku ne a makarantar Saint Academy a garin Busa Buji dake ƙaramar hukumar Jos ta Arewa, da misalin ƙarfe 11 na safe yayinda ɗalibai ke rubuta jarrabawar zango na uku. Wasu manyan ajijuwa da ke ɗaukar sama da mutane 100 ne suka ruguje inda haɗarin ya rutsa da mutane da dama. Makarantar tana kusa da gadar garin ne a yankin wani dutse da ke gafen rafi wanda wasu…
Read More

Ɗaruruwan mayaƙan Boko Haram sun tsere daga kurkuku a Jamhuriyar Nijar

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Rahotanni sun bayyana cewa, ɗaruruwan ƴan ta'adda da ɓarayi da kuma masu safarar miyagun ƙwayoyi ne suka tsere daga kurkukun Koutoukale a ƙasar Jamhuriyar Nijar. Matseretan, sun tsere ne da makamai da kuma ababan hawa bayan da suka gagari jami'an tsaron kurkukun wanda ke kusa da birnin Niamey a ranar Alhamis. Shaidu sun tabbatar da cewa, an jiyo ƙararrakin harbin bindigu da tashin bomabomai da tsakar rana inda nan-da-nan aka samu ɗaukin gaggawa daga jami'an tsaron rundunoni. Haka kuma, an ruwaito cewa matseretan sun karɓe akalar gudanar da gidan yarin inda suka yi ta nausawa ta…
Read More

Yadda matuƙin adaidata sahu ya kashe kansa kan karɓe masa babur a Legas

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wani ɗan adaidata sahu ya kashe kansa sakamakon karɓe masa babur da wasu jami'an hukuma suka yi a ƙaramar hukumar Ikorodu dake jihar Legas. Rahotanni sun bayyana cewa, lamarin ya auku ne a ranar Alhamis, 11 ga watan Yuli inda yayin da matuƙin ke tafiya kan wata hanya, sai ya yi artabu da jami'an kan wani laifi da ya aikata. Da nan ne, sai jam'ian suka karɓe adaidata sahun kana suka tafi da shi zuwa ofishinsu dake rukunin gidajen Jubilee a babbar hanyar Ikorodu-Sagamu. An samu gazawa a yunƙurinsa na zuwa karɓo babur ɗin nasa domin…
Read More

Yarjejeniyar Samoa: Son ran kafar yaɗa labarai, mummunar adawa da masu kumfar baki

Daga UMAR NURA Kafin mu kai ga bayyana ra'ayinmu game da sarƙaƙƙiyar yarjejeniyar Samoa, za mu so mu sanar da al'umma cewa, Ƙungiyar Concerned Northern Elite Forum ta masu kishin al'ummar Arewa, ba ta siyasa, kasuwanci ko jam'iyya ba ce. Manufarmu ita ce bayar da kariya ga Arewa da ma Nijeriya bakiɗaya ta hanyar gwagwarmaya da kuma yaƙar duk wani mataki ko wani al'amari da zai haifar da matsala a cikin al'umma. Kamar yadda aka sani, a ranar 28 ga Yuni, 2024 Nijeriya ta sanya hannu kan yarjejeniyar Samoa a sakatariyar ƙungiyar ƙasashen Afrika, Caribbean da Pacific (OACPS) da ke…
Read More

Jadawalin jihohin da aka haramta wa karɓar kason ƙananan hukumomi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnatin Tarayya za ta janye bai wa jihohi 20 kason ƙananan hukumomi daga watan Yuli sakamakon hukuncin cin gashin kai ga ƙananan hukumomin da kotun ƙoli ta yi a ranar Alhamis. Antoni Janar na ƙasa, Lateef Fagbemi ya wakilci gwamnatin tarayya a yayin hukuncin kotun inda ta haramta wa gwamnati raba kason ta hannun jami'an ƙananan hukumomin da aka naɗa a madadin waɗanda aka zaɓa. Mai Shari'a Emmanuel Agim wanda shi ya jagoranci shari'ar, ya bada umarnin kar a sake bada kuɗin ƙananan hukumomi ga gwamnatocin jihohinsu sakamakon yin amfani da ƙuɗaɗen ba bisa ƙa'ida ba…
Read More

Gwamnan Zamfara ya tabbatar da dokar hana zirga-zirgar babura a jihar

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya tabbatar da wata babbar dokar taƙaita zirga-zirgar babura a jihar. A ranar Alhamis ne gwamnan ya sanya hannu kan dokar a Fadar gwamnatin jihar da ke Gusau. Wata takarda da ta fito daga ofishin mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris ta bayyana cewa jami'an tsaro sun yanke shawarar taƙaita zirga-zirgar babura a jihar ne yayin wani zama na gaggawa da su ka gudanar a ranar Laraba. Sulaiman ya ce, domin tabbatar da halascin taƙaice zirga-zirgar, Antoni Janar na jihar, Abdul'aziz Sani (SAN) ya gabatar da dokar mai lamba ta…
Read More