11
Jul
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tsige Daraktan kamfanin buga kuɗi (NSPM), Ahmed Halilu tare da wasu manyan ma'aikata guda huɗu. Ahmed Halilu, ɗan uwa ne ga Aisha Buhari, matar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari wanda aka naɗa a watan Satumban 2022 a lokacin gwamnatin Buhari. Sauran waɗanda aka tsige sun haɗa da; Ado Ɗanjuma, Daraktan harkokin rijistar masana'antu; Chris Orewa, Daraktan gudanarwa reshen jihar Legas; Tunji Kazeem, Daraktan kundaddakin tsaro; da Victoria Irabor, Sakatariya, wacce matar Janar Lucky Irabor ce, tsohon shugaban harkar tsaro. Daraktan gudanarwa reshen Abuja, Abubakar Minjibir shi ne babban Darakta na…
