08
Jul
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Kotun ɗaukaka ƙara reshen jihar Ribas, ta kori ƙararraki biyu da shuwagabannin ƙananan hukumomi da ke ɓangaren tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike suka shigar bayan da ta ce ba su cika ƙa'idojin sauronsu ba. Hon. Enyiada Cookey-Gam da wasu mutum shida suka shigar da su masu ɗuake da lambobi kamar haka; CA/PH/137M/2024 da kuma CA/PH/145M/2024 inda a ciki su ke ƙalubalantar karamar kotu kan hukuncinta na ƙara wa'adin shugabancin majalisar da suka nema. Kotun ɗaukaka ƙarar ta ce ƙalubalen nasu basu gamsar da tsare-tsaren doka ba don haka, ta yi watsi da su. Ɗaya daga cikin…
